24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Ashe Lilin Baba yana da wata matar kafin aurensa da Ummi Rahab

LabaraiKannywoodAshe Lilin Baba yana da wata matar kafin aurensa da Ummi Rahab

Bayan an sha shagalin auren Mawaki Lilin Baba da Jaruma Ummi Rahab, akwai wasu al’amura masu ban mamaki da su ka auku yayin auren, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Tabbas babu inda aka ji Mawakin ya ce ba ya da wata matar, amma kuma yawancin mutane sun yi zaton Ummi ce matarsa ta farko musamman ganin yana da karancin shekaru.

Abinda jama’a basu fahimta ba shi ne, Lilin Baba mutum ne wanda bai fiya bayyana abubuwa da dama dangane da kansa ba.

Tashar Tsakar Gida ta bayyana cewa Mujallar Fim ta shaida yana da mata da da daya, sai dai duk yadda ku ke da shi ba zai taba nuna maka matarsa ta farko ba.

Yayin da aka kai Ummi gidan da ya ajiyeta a Kaduna, an tarar da tagwayen gidaje biyu iri daya, wanda dayan matarsa ta farko ne ciki, na biyun kuma Ummi Rahab.

Muna yi musu fatan samun zaman lafiya da zuri’a dayyiba. Sannan muna fatan Allah ya kade fitintinu dag auren nasu. Ameen.

Alkawari ya cika: An daura auren Jaruma Ummi Rahab da Mawaki Lilin Baba

A ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekarar 2022, Jarumin Kannywood kuma mawaki Lilin Baba ya auri jaruma mai tasowa, Ummi Rahab.

Shafin Arewafamilyweddings ya bayyana bidiyonta sanye da fararen kaya ta dauki kwalliya irin ta amare inda a kasa aka bayyana cewa an daura aurenta da Lilin Baba.

Kamar yadda labarai su ka dinga yawo, jarumin ya daura aniyar aurenta tun shekarar da ta gabata, amma bisa wasu dalilai aka dinga jinkirta auren.

Wasu kuma gani su ke yi tamkar shirin fim ne soyayyar tasu kamar yadda su ka bayyana a shirin “Wuff” mai dogon zango.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe