27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Shugaba Buhari ya zaɓi sabbin ministoci 7, sanatoci 3 sun bar APC

LabaraiShugaba Buhari ya zaɓi sabbin ministoci 7, sanatoci 3 sun bar APC

Majalisar dattawa ta ƙarbi jerin sunayen mutum bakwai domin zama ministoci waɗanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aike mata da su domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin ministoci.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa roƙon yana cikin wata wasiƙa da aka aika ga shugaban majalisar, Ahmad Lawan, wacce kuma aka karanta a zauren majalisar a farkon zaman majalisar na ranar Talata.

Shugaba Buhari a cikin wasiƙar yayi bayanin cewa roƙon yana kan turbar sashi 147 (2) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

Sunayen sabbin ministocin da shugaba Buhari ya zaɓa

Waɗanda aka zaɓa sun haɗa da, Henry Ikoh – jihar Abia; Umana Umana – jihar Akwa Ibom; Ekumankama Nkama – jihar Ebonyi; da kuma Goodluck Opiah – jihar Imo.

Sauran sun haɗa da, Umar El-Yakub – jihar Kano; Ademola  Adegoroye – jihar Ondo; da kuma Odum Odi – jihar Ribas.

An samu gurbi a cikin ministoci tun lokacin da wasu tsofaffin ministoci su kayi murabus daga kan muƙaman su domin tsayawa takara.

Waɗanda su kayi murabus ɗin sun haɗa da tsohon ƙaramin ministan ilmi, Chukwuemeka Nwajiuba; tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon ministan haƙo ma’adanai da ƙarafa, Uche Ogah; tsohon ministan yankin Neja Delta, Godswill Akpabio; da kuma tsohon ƙaramin ministan yankin Neja Delta, Sanata Tayo Alasoadura.

Sanatoci uku sun fice daga APC

Haka kuma, sanatoci uku na jam’iyyar APC sun fice daga jam’iyyar mai mulki a ƙasar nan.

Sanata mai wakiltar Katsina ta arewa, Ahmad Babba-Kaita da Sanata mai wakiltar Edo ta arewa, Francis Alimikhena, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP; yayin da Sanata Lawal Gumau, ya koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)

Shugaban majilasar shine ya karanta wasiƙun su na ficewa da sauya sheƙa a zaman majalisar na ranar Talata.

Buhari yana shirin dakatar da amfani da kalanzir da itace a Najeriya

A wani labari na daban kuma, shugaba Buhati na shirin dakatar da amfani da kalanzir da itace a ƙasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya sabon shiri akan dakatar da amfani da kalanzir a kasarnan zuwa shekarar 2030, LIB ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a wani taron yanar gizo da suka yi da shugaban kasar Amurka, Joe Biden akan Major Economies Forum on Energy and Climate Change (MEF), inda ya ce hakan na cikin shirin da zai taimakawa Najeriya wurin samar da yanayi mai kyau.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe