24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Buhari yana shirin dakatar da amfani da kalanzir da itace a Najeriya

LabaraiBuhari yana shirin dakatar da amfani da kalanzir da itace a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya sabon shiri akan dakatar da amfani da kalanzir a kasarnan zuwa shekarar 2030, LIB ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a wani taron yanar gizo da suka yi da shugaban kasar Amurka, Joe Biden akan Major Economies Forum on Energy and Climate Change (MEF), inda ya ce hakan na cikin shirin da zai taimakawa Najeriya wurin samar da yanayi mai kyau.

Channels Television ta ruwaito cewa shugaban kasan ya lissafo hanyoyin da za a tabbatar an dage wurin amfani da motocin haya a matsayin salon zirga-zirgar mutane, inda ya ce za a samu ragi akan yawan kona shukoki zuwa shekarar 2030.

Ya bayyana cewa NDC salo ne na kawo gyaran yanayi ne wanda majalisar dinkin duniya ta samar, kuma zuwa ranar 27 ga watan Mayun 2021 aka amince da bin wadannan ka’idojin.

A shekarar 2012, gwamnatin tarayya ta shirya sabon salon da aka fi sani da National Strategic Policy na LPG tare da hadin kan masu masana’antar danyen man fetur.

Kuma hakan zai taimaka ne wurin dakatar da amfani da kalanzir da itace a kasar nan, kowa ya koma amfani da sinadarin gas.

Kuma ana sa ran nan da shekaru 10 abin zai tabbata.

Buhari ya umarci TikTok da sauran kafafe su cire duk wata wallafar tsiraici ciki awanni 24

Gwamnatin Tarayya karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bai wa duk manyan kafafen sada zumuntar zamani kamar Instagram, Facebook, Twitter, WhatsApp da TikTok umarnin cire duk wata wallafa mai dauke da tsiraici, lalata ko kuma wani abu na rashin da’a cikin awanni 24, Instablog9ja ta ruwaito.

An samu wannan bayanin ne cikin sabbin dokokin amfani da kafafen sada zumunta ko yanar gizo da aka saki.

Kamar yadda dokar ta nuna:

“Duk wadannan kafafen na yanar gizo su yi gaggawar cire duk wasu wallafe-wallafe da ke dauke da tsiraici, lalata da sauransu wadanda aka shirya don tozarta mutane.

“Wajibi ne kafafen su dinga kula da korafi wurin sauke duk makamanciyar wallafar tsiraici cikin awanni 24.”

Dokar ta kuma bayar da umarnin a cire duk wata wallafa da ke kalubalantar wani ko kuma hukumar da ke karkashin gwamnatin tarayya.

Har ila yau gwamnati ta umarci kafafen da su tabbatar ba a sake wata wallafa makamanciyar hakan ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe