23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Mu ba mabarata ba ne, yunwa ba za ta tilasta mu komawa ba, ASUU ga Gwamnatin Tarayya

IlimiMu ba mabarata ba ne, yunwa ba za ta tilasta mu komawa ba, ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Shugabannnin Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU sun bayyana cewa su ba mabarata ko maroka bane, don gwamnati ta dakatar da albashinsu, hakan ba zai tilasta su dakatar da yajin aikin da su ka tafi ba, LIB ta ruwaito.

A ranar 14 ga watan Fabrairu, bayan gwamnatin Tarayya ta gaza cimma bukatunsa su ka tafi yajin aikin jan kunne na wata daya. Daga nan su ka kara makwanni 8 wanda daga bisani su ka tafi yajin aikin sai baba ta gani.

Sun ci gaba da yajin aikin wanda gwamnatin tarayya ta dakatar da albashinsu tun daga nan. Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ya ce hakan ya yi daidai da umarnin da sashi na 43 da dokar kwadago ta tanadar.

A wata takarda wacce shugaban ASUU na kasa ya saki ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, Emmanuel Osodeke, ya yabawa mambobin kungiyar akan yadda su ka jajirce da yajin aikin duk da gwamnatin tarayya ta dakatar da albashinsu.

A cewarsa:

“Yayin da mu ke ci gaba da fafutuka, mun yaba da yadda mambobinmu su ka jajirce wurin dagiya da ganin kawo ci gaba da tsarin Jami’o’in kasar mu.

“Muna yabawa mambobinmu akan tsayarwarsu tsayin daka duk da wahalar da su da iyalansu ke ciki sakamakon rashin albashi. Hakan ya nuna kenan mu ba mabarata bane, kuma yunwa ba za ta dakatar da mu daga yajin aikin ba.

“Jajircewarmu ta sanya gwamnati ta zauna don tattaunawa da mu. Mun yi taro kashi biyar da gwamnatin tarayya sannan mun yi taro biyu da ministan ilimi. Yarjejeniyar ASUU ga gwamnatin tarayya ta 2009 tana ta tafiya cikin tsanaki. Sai dai wajibi ne mu ci gaba da dagewa.

“An kara gwada UTAS din da mu ka gabatar a karo na uku, da kuma UPS, za a fara gwada IPPIS mako mai zuwa. Muna shirin samun nasara. Mu ci gaba da hada kai da kungiya. Wadanda kan su a hade yake ba za a taba cin galaba akansu ba.”

Yajin aikin ASUU shi ne mafita don ceto ilimin Najeriya daga rugujewa gaba ɗaya – Tsohon Shugaban Ƙungiyar

Farfesa Abiodun Ogunyemi, tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ya zargi masu riƙe da madafun iko da lalata fannin ilimi a Najeriya bisa tsariDaily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a safiyar Talata da gidan Talabijin na Channels, ya ce yajin aikin ASUU mafita ce ta ceto ilimin ƙasar nan daga rugujewa gaba ɗaya.

A wata sanarwa da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin baiwa gwamnati isasshen lokaci domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta cikin gamsuwa.

Wasu daga cikin buƙatun ASUU sun hada da sakin kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i, sake tattaunawa kan yarjejeniyar FGN/ASUU na shekarar 2009, sakin kutdaden alawus-alawus ga malaman jami’o’i, da tura tsarin biyan UTAS na biyan albashi da alawus-alawus na malaman jami’o’i.

Amma Ogunyemi ya ce, “Babban batun shi ne muna son ceto ilimin Najeriya saboda abin da masu mulki ke yi shi ne lalata fannin ilimi bisa tsari”.

Sun lalata makarantun firamare da sakandare na gwamnati kuma abin da masu mulki ke kai wa a yanzu shi ne jami’o’in gwamnati da makarantun gwamnati baki daya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe