28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda saurayi ya titsiye budurwarsa a dakin otal su na cin amarsa da abokinsa

LabaraiYadda saurayi ya titsiye budurwarsa a dakin otal su na cin amarsa da abokinsa

Wani dan Najeriya ya titsiye budurwarsa a dakin otal inda yake zargin ta tare ne don cin amanarsa da abokinsa, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, budurwar ta shiga tashin hankali bayan saurayin ya kamata dumu-dumu tare da abokin nasa a dakin otal din.

Ya nuna rashin jindadinsa akan wannan abu da budurwarsa tayi, yayin da yake bayyana irin kokarin da ya dade yana yi mata.

Sai dai babu tabbas akan cewa ba shirya lamarin yayi ba tare da abokinsa wanda yake cikin dakin.

Ga bidiyon a kasa:

Saurayina ya ce in ban ba shi kai na ba, zai koma bin karuwai da shaye-shaye, Budurwa

Wata budurwa ta nemi shawarar jama’a akan wani sharadi da saurayinta ya ba ta. A cewarta, har gida ya zo ya sanar da ita tsarinsaDaily Trust Hausa ta ruwaito.

Ta ce ya bukaci ya ba ta kanta idan ba haka ba zai fita waje ya dinga neman karuwai ko kuma shaye-shaye wanda da ma abokansa sun dade a cikin harkar.

A yadda ta nuna, ba ta son ba shi kanta sannan ba ta son rabuwa da shi, hakan ya sa ta bazama neman mafita.

Ta ci gaba da cewa:

“Saurayina ne ya ke zuwa min da wasu tsare-tsare duk lokacin da ya zo gidanmu.

“Ya ce ko dai in amince da bukatarsa ko kuma idan har na ki yarda zan koma bin karuwai da kuma shaye-shaye saboda dama abokansa sun dade a harkar, shi ne kadai Allah ya tsare.

“Ya ce in har na ki yarda da bukatarsa, karuwai zai koma bi. Don Allah ‘yan uwan na san dai ba zan amince ba amma ya ku ke gani ya kamata in yi?”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe