27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Alkawari ya cika: An daura auren Jaruma Ummi Rahab da Mawaki Lilin Baba

LabaraiKannywoodAlkawari ya cika: An daura auren Jaruma Ummi Rahab da Mawaki Lilin Baba

A ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekarar 2022, Jarumin Kannywood kuma mawaki Lilin Baba ya auri jaruma mai tasowa, Ummi Rahab.

Shafin Arewafamilyweddings ya bayyana bidiyonta sanye da fararen kaya ta dauki kwalliya irin ta amare inda a kasa aka bayyana cewa an daura aurenta da Lilin Baba.

Kamar yadda labarai su ka dinga yawo, jarumin ya daura aniyar aurenta tun shekarar da ta gabata, amma bisa wasu dalilai aka dinga jinkirta auren.

Wasu kuma gani su ke yi tamkar shirin fim ne soyayyar tasu kamar yadda su ka bayyana a shirin “Wuff” mai dogon zango.

Sai dai daga baya kuma aka samu tabbacin auren kasancewar ko wannensu ya wallafa katin auren sannan su na yawaita yi wa juna tsokaci da kalaman soyayya.

Tashar Tsakar Gida ta bayyana cewa har akwatinan aure ya kai gidansu jarumar inda daga nan aka fara shagulgula.

A jiya hotunan Kamun amarya su ka bayyana wanda ta dinga rawa tare da kawayenta cike da farin ciki.

za bride
Alkawari ya cika: An daura auren Jaruma Ummi Rahab da Mawaki Lilin Baba

Idan ba a manta ba, a baya uban gidanta a masana’antar, Adam Zango, ya nuna ra’ayin aurenta, sai dai bata amince ba.

Lamarin da ya dinga janyo kananun maganganu ta ko ina har aka dinga musanta asalinta. Daga bisani yayanta kuma marikinta, Yasir Ahmed ya bayyana hotunan iyayenta inda ya tabbatar suna Saudiyya.

A ummarar shekarar nan Labarun Hausa ta bayyana yadda jarumar da mahaifiyarta su ka hadu inda su ka dinga kuka kasancewar sun dade rabonsu da juna.

Sai dai dama yayanta ya ce babu dadewa idan ta dawo daga Saudiyya za a daura aurensu da Lilin Baba.

Muna musu fatan alkhairi da kuma samun kwanciyar hankali da zuri’a dayyiba. Ameen.

An sa ranar auren Lilin Baba da jaruma mai tasowa, Ummi Rahab

Yayin da mutane suke ta jita-jita da surutai akan cewa ‘yan fim ba sa auren junan su, Lilin Baba da Ummi Rahab zasu karya wannan rantsuwar ta’yan fim ba sa auren juna, don yanzu haka an sanya ranar auren su.

A rana Juma’a, 4 ga watan Maris Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa batun sa ranar auren nasu.

Yanzu haka duk wasu shirye-shirye sun kankama akan cewa Lilin Baba zai angwance da amaryarsa, Ummi Rahab bayan sallah mai zuwa.

Tashar Tsakar Gida ta samu labari akan cewa manyan jarumai kamar Ali Nuhu ne suka shige wa mawakin gaba akan neman auren auren Ummi kuma an ba su auren ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe