28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kaso 98% na mazan Najeriya masu aure, su na da ‘yan matansu a waje, Boma

LabaraiKaso 98% na mazan Najeriya masu aure, su na da 'yan matansu a waje, Boma

Jarumin shirin gida talabijin na BBNaija, Boma Akpore ya ce kaso 98 bisa dari na mazan aure da ke kasar Najeriya su na da ‘yan matansu a waje baya ga matansu na aure, LIB ta ruwaito.

Boma ya bayyana hakan ne a wani shirin taron BBNaija na “Shine Ya Eye” wanda aka bayyana ranar 16 ga watan Yunin 2022.

Kamar yadda yace:

“Kaso 95% na mazan Najeriya masu aure suna da ‘yan matansy a waje, kila ma kaso 98.

“Zan fadi abinda mutane dayawa suke tsoron fadi. Kaso 98% na mazan Najeriya masu aure suna da ‘yan mata. Wa kuke tunanin yana daukar nauyin ‘yan matan?

“Kusan ko wanne namiji mai aure yana da budurwarsa. Duk ‘yan mata nan, abubuwan da suke siya duk maza masu aure ne ke siya musu.”

Daga neman magani: Mai maganin gargajiya ta mallake matar aure, ta tatse kudadenta tare da bautar da ita

Ana zargin wata mai maganin gargajiya, Hauwa da rikidewa ta koma amfani da sihiri wurin tatse wata matar aure wacce ta je neman magani a wurinta kasancewar mijinta ba ya da lafiya, Dala FM ta ruwaito.

Kamar yadda matar ta shaida, har sadakin auren diyarta sai da ta amshe sannan ta sanya ta ta sayar da gonarta ta mika mata kudaden.

Ta ci gaba da bayyana cewa har tura yaranta gidan matar take yi su na yi mata wanki mai yawan gaske da aikace-aikace.

Dakyar ta samu Allah ya kwace ta daga hannun matar, hakan ya sa ta bayyana gaban kotu don a nema mata hakkinta.

“Ita Hauwa ta cuce ni. Da zimmar cewa zata taimake ni mai gidana ba lafiya. Tun daga lokacin da naje neman magani ta mallake ni ni da yarana. Duk abinda tace mu yi shi muke yi babu makawa.

“Idan ta ce ma kar ka kula mahaifiyar da ta haifeka ma baza ka kulata ba. Atamfofi, ta ce Mai Dawa ya ce a kawo atamfofi. Omo ta ce azo ayi mata wanki. Wallahi sai yarana su yi mata wanki sai su yi mata wanki mai yawa kamar omo ukun nan da ake siyarwa N110. Girki, aike, ta dai mayar damu kamar bayinta.

“Lokaci guda Ubangiji Allah ya bani damar in yi magana akan cutar da ta yi min. Shi kanshi filin da ta sanya na siyar kudin ita na mika mawa. Ba za ta cuce ni ba, duk lokacin da na nema ba za ta hana ni ba. Idan nayi magana ta ce an tafi da kudin Abuja, anje da shi Saudiyya.”

Ta bayyana yadda take hada ta da iska wadanda za su razana ta da sunan zasu kassara ta da yaranta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe