28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Buhari ya umarci TikTok da sauran kafafe su cire duk wata wallafar tsiraici ciki awanni 24

LabaraiBuhari ya umarci TikTok da sauran kafafe su cire duk wata wallafar tsiraici ciki awanni 24

Gwamnatin Tarayya karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bai wa duk manyan kafafen sada zumuntar zamani kamar Instagram, Facebook, Twitter, WhatsApp da TikTok umarnin cire duk wata wallafa mai dauke da tsiraici, lalata ko kuma wani abu na rashin da’a cikin awanni 24, Instablog9ja ta ruwaito.

An samu wannan bayanin ne cikin sabbin dokokin amfani da kafafen sada zumunta ko yanar gizo da aka saki.

Kamar yadda dokar ta nuna:

“Duk wadannan kafafen na yanar gizo su yi gaggawar cire duk wasu wallafe-wallafe da ke dauke da tsiraici, lalata da sauransu wadanda aka shirya don tozarta mutane.

“Wajibi ne kafafen su dinga kula da korafi wurin sauke duk makamanciyar wallafar tsiraici cikin awanni 24.”

Dokar ta kuma bayar da umarnin a cire duk wata wallafa da ke kalubalantar wani ko kuma hukumar da ke karkashin gwamnatin tarayya.

Har ila yau gwamnati ta umarci kafafen da su tabbatar ba a sake wata wallafa makamanciyar hakan ba.

Tsohon bidiyon Fasto Tunde Bakare yana ce wa mambobin cocinsa Ubangiji ya nuna masa zai maye gurbin Buhari a 2023

An samu tsohon bidiyon Fasto Tunde Bakare yana sanar da mambobin cocinsa cewa shi ne zai dar kujerar shugabancin Najeriya bayan Buhari, LIB ta ruwaito.

Yayin da ya ke wa’azi a cocin a ranar, faston ya kada baki ya ce:

“Ku fada a duk inda ku ke son fadi. Idan kun taba ji a wani wuri, ina maimaita muku cewa in dai a siyasar Najeriya ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne shugaban kasar nan na 15, ni ne zan zama na 16.

“Ban taba fada muku ba a baya. Amma a yau na bayyana muku, da safiyar nan ina sanar da ku cewa babu abinda zai sauya wannan maganar da yardar Jesus.”

Fasto Bakare ya biya N100m na kudin fom din takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC amma bai samu kuri’a ko guda daya ba a wannan zaben fida da gwanin da aka gama.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe