22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Na tsine wa Peter Obi, ba zai ci zabe ba tunda makwado ne, ba ya taimako, Fasto Mbaka

LabaraiNa tsine wa Peter Obi, ba zai ci zabe ba tunda makwado ne, ba ya taimako, Fasto Mbaka

Fitaccen faston Katolika kuma darektan Adoration Ministry Enugu Nigeria (AMEN), Fr Mbaka ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya, Peter Obi, ba zai taba zama shugaban kasa ba.

Mbaka ya shawarci ‘yan Najeriya da su marawa Atiku baya inda yace ya mayar da hankali wurin neman shugabanci kwarai don haka su share Peter Obi.

Kamar yadda shafin Daily Mail Gist ya bayyana a ranar 15 ga watan Yunin 2022, Fr Mbaka ya ce Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba.

Sun shaida yadda Mbaka ya jero dalilansa akan batunsa na cewa Peter ba zai ci zabe ba. Ya ce idan aka duba yadda Peter Obi ya kasance mutum mai mako kuma baya taimakon wasu.

Ya ce Peter Obi yana da mako kuma dakyar yake taimakon mutane don haka gara ya zabi tsohon da zai taimakawa jama’a akan ya zabi matashi kamar Peter Obi marar taimako. Ya nemi a zabi Tinubu ko kuma Atiku.

Ya ci gaba da shaida yadda ya taimaki Peter Obi har aka mayar da shi matsayinsa lokacin da aka cire shi daga kujerar gwamnan Jihar Anambra amma bai taba tunanin tallafa masa ba.

Yayin bayani akan takarar Atiku a matsayin shugaban kasar Najeriya, Mbaka ya ce a manta da batun Peter har dai ya shiya yin takara.

Ya shaida yadda Peter ya kasance makwado a lokacin da yake kamfen wanda a tunaninsu zai tattala dukiyar Jihar Anambra idan ya ci zabe.

Mbaka ya ci gaba da cewa:

“Na tsinewa Peter Obi, babu inda zai je in har bai zo gabanmu ya duka don nema albarkarmu ba.”

Sojan Najeriya ya halaka kan sa bayan an cafke shi bisa taimakawa ‘yan ta’addan ISWAP

Wani sojan Najeriya wanda aka cafke bisa laifin haɗin guiwa da ‘yan ta’addan ISWAP, ya halaka kan sa yayin da ake tusa ƙeyar sa zuwa barikin sojoji. Jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Sojan na da hannu a cikin hare-haren baya-bayan nan

PRNigeria ta samu cewa sojan wanda yake tare da ɗaya daga cikin bataliyoyin sojin Najeriya da ke a yankin Arewa maso gabas, ɓangaren masu leƙen asiri ya gano cewa yana da hannu dumu-dumu a hare-haren kwana-kwanan nan da aka kai a wasu gidajen karuwai da mashaya barasa.

Yana da hannu a hare-haren da aka kai kwanan nan a garuruwan Geidam da Gashua cikin jihar Yobe

An cafke shi ne yayin da yake ƙoƙarin arcewa bayan ya fahimci cewa jami’an ɓangaren masu leƙen sirri gano duk wani motsin sa da yake yi da ‘yan ta’adda.

Ya ƙwaci bindiga sannan ya halaka kan sa

Bayan an sanya masa ankwa, cikin hikima ya ƙwace bindiga daga wajen ɗaya daga masu rakiyar sa sannan ya halaka kan sa.

Haka kuma, ana cigaba da gudanar da bincike domin ganin an cafke sauran waɗanda ake zargin suna da  hannu a cikin sojojin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe