24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki

LabaraiMajiyoyi masu ƙarfi sun bayyana wanda Tinubu zai ɗauka a matsayin mataimaki

Dukkanin wasu alamu sun gama nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, zaa ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa na ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Majiyoyi masu ƙarfi waɗanda ke da alaƙa da tarurrukan da ake yi kan lamarin fitar da mataimakin su ka shaidawa jaridar Vanguard a jiya Laraba.

APC za ta tsayar da musulmi da musulmi takara

Majiyoyin sun ce jam’iyyar APC za ta tsayar da musulmi da musulmi ne a zaɓen shugaban ƙasa.

shettima
Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima. Hoto daga jaridar Vanguard.

Da aka tambaye su dangane da damar da gwamnan jihar Filato yake da ita, wanda kirista ne, ɗaya daga cikin majiyoyin yace ‘wasu mutane ne kawai ke da wannan shawarar. Tinubu ba zai iya yin takara tare da Lalong ba.

Ya ƙara da cewa wasu na hannun daman Tinubu, sun yi amanna cewa Shettima, wanda yasan burin takarar Tinubu sosai da sosai shi yakamata ya samu kujerar.

Baa gama tabbatar da wanda Tinubu zai zaɓa ba

Da aka tambaye shi ko zaɓin Shettima ya kammalu, majiyar sai ya kada baki yacce:

Ba abinda ya kammala har yanzu. Sunan shi yana cikin sunayen da ake dubawa. Sunayen sauran ba su kai yawan yadda ake faɗin na Shettima ba.

Irin su Boss Mustapha duk ana duba su. Shettima shine zaɓin farko.

A cewar majiyar

Hakan na zuwa ne dai bayan mai tsawatar wa na majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, yace babban zaɓin da Tinubu yake da shi shine ya ɗauki musulmi a matsayin mataimakin sa domin samun damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Kwararan ‘yan siyasa guda  uku 3 na Arewa  wadanda ake hasashen Tunibu zai iya daukar dayan su mataimaki

A wani labari na daban kuma, mun kawo muku ƙwararan ‘yan siya uku na Arewacin Najeriga wanda ake hasashen Tinubu ɗaukar mataimaki a cikin su.

Yayin da kakar zaben shugaban kasa ke karatowa a shekarar 2023, yan siyasa a jamiyyar APC mai mulki, na ci gaba da neman takarar mataimakin shugaban kasa, bayan kammala zaben fidda gwani na da jamiyyar ta gudanar, wanda Asiwaju Bola Ahmad Tunibu ya yi nasarar zama dan takarar, gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2023. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe