23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An cafke tsoho mai shekaru 80 bisa laifin yin fyaɗe ga yarinya ‘yar shekara 11 a Borno

LabaraiAn cafke tsoho mai shekaru 80 bisa laifin yin fyaɗe ga yarinya 'yar shekara 11 a Borno

Jami’an ‘yan sandan jihar Borno sun cafke wani tsoho mai shekaru 80, Saleh Bukar, bisa laifin yin fyaɗe ga wata ƙaramar yarinya mai shekaru 11 a duniya.

Yayi wa yarinyar fyaɗe a lokuta da dama

Shafin LIB ya rahoto cewa, da yake tasa ƙeyar wanda ake zargin a gaban manema labarai ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, 2022, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar, yace yayar yarinyar ce mai suna Falmata Ali, ta lura da aukuwar lamarin bayan taga wani irin ruwa na fitowa a gaban yarinyar. A cewar ta daga baya yarinyar ta faɗi mata gaskiya inda tace Bukar yayi mata fyaɗe sau da dama a lokuta daban-daban.

An kama wasu mutanen daban bisa laifin aikata fyaɗe

Haka kuma kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, hukumar su ta cafke wasu mutum 6 bisa laifin yin fyaɗe ga wata yarinya mai shekaru 13. Yace an cafke su ne a wurare daban-daban cikin jihar.

Ya bada sunayen mutum shidan kamar haka, Lawan Nasiru, mai shekaru 43, Musa Tukur, mai shekaru 50, Samaila Hassan, mai shekaru 60, da Garba Suleiman, mai shekaru 60.

Yace waɗanda ake zargin, mazauna yankin Hausari cikin birnin Maiduguri, sun yaudari yarinyar zuwa wata maɓoya sannan su ka yi amfani da ita. Umar yace sun yaudari yarinyar ne da kuɗi, kimanin N200 zuwa N500 domin yin amfani da yarinyar a lokuta daban-daban.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da zaa tura waɗanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Kotu ta tura wasu gardawa biyu gidan gyaran hali bisa ɗirkawa yarinya ‘yar shekara 13 fyaɗe

A wani labari na daban kuma, an tura wasu mutum biyu gidan kaso bisa yin fyaɗe ga yarinyar ‘yar shekara 13 a duniya.

Wata kotun majistare ta Ikeja a jihar Legas ta tura wasu mutum biyu masu suna Sakiru Oladosu, mai shekaru 50, da Tola Rasaq, mai shekaru 40, gidan gyaran hali bisa laifin yin fyaɗe da ɗirkawa wata yarinya mai shekaru 13 a duniya ciki.

Mutum biyun da ake zargi waɗanda kuma su ka kai yarinyar wajen zubar da ciki bayan sun yi mata wannan ɗanyen aikin, suna rayuwa ne a yankin Mushin cikin Legas

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe