23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda wasu ma’aikatan gidan gona su ka jefa gawar maigidan su a rijiya bayan sun halaka shi a Abuja

LabaraiYadda wasu ma'aikatan gidan gona su ka jefa gawar maigidan su a rijiya bayan sun halaka shi a Abuja

‘Yan sanda a Abuja sun bayyana yadda ma’aikatan gidan gonan wani manomi, Hussaini Aliyu Takuma, su ka halaka shi sannan su ka jefa gawar sa cikin wata rijiya kusa gonar sa a ƙauyen Jeida, cikin ƙaramar hukumar Kuje, a Abuja.

An jefa gawar sa cikin rijiya bayan an halaka shi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa manomin ya ɓace ne a gonar sa a ranar 2 ga watan Yuni, 2022, sai dai bayan gudanar da kwakkwaran bincike an samu cewa kashe shi akayi sannan aka jefa gawar sa cikin rijiya.

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mataimakin kakakin hukumar ‘yan sandan Abuja, ASP Oduniyi Omotayo, yayi bayanin cewa an kama waɗanda ake zargi da kisan a yankin Kabusa, yayin da su ka kama hanyar Kano da dabbobin mai gidan na su.

Omotayo yace ana cigaba da gudanar da bincike sannan zaa bayyana sakamakon binciken da zaran an kammala.

Ya ƙara da cewa:

Ɗan’uwan mamacin ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda na Kuje, a ranar 4 ga watan Yuni, 2022, cewa ɗan’uwan sa ya tafi gonar sa ranar 2 ga watan Yuni, 2022 kuma bai dawo ba.

Nan da nan ‘yan sanda su ka duƙufa aiki, inda su ka tura jami’an bincike kan ƙorafin. An kama mutum biyu waɗanda ma’aikatan mamacin ne a yankin Kabusa, yayin da su ka nufi Kano da dabbobin mamacin da su ka sace.

Bayanan da aka samu a hannun waɗanda ake zargin ya sanya aka gano gawar mamacin cikin wata rijiya a kusa da gonar sa. Ana cigaba da gudanar da bincike domin gano abubuwan da su kayi silar mutumar mamacin.

Waɗanda ake zargin dai an samu cewa sun tafi da aƙalla tumakai guda 40, da awakai guda 6, bayan sun kashe mai gidan na su.

Wata matar aure da ‘ya’yan ta sun biya N120,000 a halaka mahaifin su domin cin dukiyar sa

A wani labari na daban kuma, wata matar aire tare da ‘ya’yan ta sun biya maƙudan kuɗi domin a halaka mahaifin yaran saboda samun damar cin dukiyar sa.

Yan sanda a jihar Adamawa sun cafke wata matar aure mai suna, Hafsat Saidu, da ‘ya’yan ta biyu, Faisal Saidu da Fa’iza Saidu, bisa zargin haɗa baki wajen biyan N120,000 domin a halaka mahaifin su, Saidu Mamman, mai shekaru 60 a duniya.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, wanda ya tabbatarwa da shafin LIB aukuwar lamarin, ya ce lamarin ya auku ne a gidan su dake a  Sangere FUTY cikin ƙaramar hukumar Girei ta jihar, a ranar 22 ga watan Afrilun 2022.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe