27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Akwai yuwuwar Jaruma Ummi Alaqa ta maye gurbin Nafisat Abdullahi a shirin Labarina

LabaraiKannywoodAkwai yuwuwar Jaruma Ummi Alaqa ta maye gurbin Nafisat Abdullahi a shirin Labarina

Bisa dukkan alamu, jarumar shirin fim din Alaka, Habiba Aliyu, wacce aka fi sani da Ummi Alaqa ce zata maye gurbin Nafisat Abdullahi a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

LabarunHausa ta gano hakan ne bayan bibiyar shafin jarumar wacce ta hada hotonta da na Nafisat Abdullahi inda ta ke tambayar mabiyanta akan wacce rawa za ta taka idan ta maye gurbin Nafisat a shirin fim din.

Idan ba a manta ba, shirin ya yi matukar farin jini wanda an kwararo kammala Zango na biyu jarumar suka samu matsala da mashiryin shirin, Naziru Sarkin Waka da kuma darektan shirin, Malam Aminu Saira, daga nan shirin ya tsaya cak.

Sai dai kamar yadda Baban Chinedu ya shaida a wani bidiyo da yayi ana tsaka da rikicin Nafisat da Naziru, ya ce saboda rashin ihsani ne tsakanin mashirya shirin da kuma jaruman ya sanya su ka dakata daga ci gaba.

Amma a bangaren Nafisa, tun bayan dakatarwarta ta saki wata takarda wacce ta ke baiwa mutane hakuri akan cewa akwai abubuwa masu matukar muhimmanci da suka sha gabanta, wadanda su ne zasu dakileta daga ci gaba da shirin.

“Shin wacce irin rawa kuke ganin zan taka a gurbin Sumayya cikin shirin Labarina Series.”

A ranar Lahadi, jaruma Ummi ta yi wallafa a shafinta na Instagram bayan ta hada hotonta da na Nafisat Abdullahi, daga nan tace:

Nan da nan mutane suka bazama suna ta tsokaci karkashin wallafar, wasu suna ganin zata taka babbar rawa, yayin da wasu suke ganin gogewarta bata kai ta maye gurbin Sumayya ba.

Tsokacin jama’a karkashin wallafar

LabarunHausa ta tattaro wasu daga cikin tsokacin mutane:

t_jega ya ce:

“Ina miki fatan kiyi abinda yafi nata kyau. Allah ya kara daukaka.”

real_ab_yareema ya ce:

“Bisa yadda takardar tazo, shirin bai dace da ke ba. Shekarunki basu kai ba. Kalar fatarku ta zo daya. Duk da cewa an canja fuskarta amma ai ba a canja girman jiki da murya ba. Ya dace ace an yi canjin yadda ya dace.”

tukur_ms ya ce:

“Mu dai masoya shirin Labarina mai dogon zango ne. Allah ya bada sa’a.”

its_young_writer ya ce:

“Abin ma be yi tsari ba. Ke kina karamarki a saki matsayin mai shekaru 30 da doriya.”

Dalilin cire Ummi Alaqa ba zai fadu ba, zai iya taba mutuncinta, Jarumi Ali Nuhu

Dangane da shiri mai dogon zango na Alaqa wanda ya dauki hankalin jama’a da dama a makon nan bayan ganin an sauya jaruma wacce tauraronta ya fara haskawa, Habiba Y Aliyu wacce aka fi sani Ummi Alaqa ya bata wa masu kallo rai, Ali Nuhu ya magantu.

Mutane sun dinga surutai akan sauya jarumar inda wasu suke ganin saboda Maryam Yahaya ta fi ta fada ne a kamfanin yayin da wasu ke ganin kamar bakin ciki ake yi wa jarumar shiyasa aka cire ta aka mayar da Maryam.

Mutane da dama sun dinga surutai kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Bayan ganin hakan ne yasa Tashar Tsakar Gida ta yi tattaki don samun mai shirya shirin kuma mai bayar da umarnin shirin, Ali Nuhu don jin albarkacin bakinsa.

Jarumi Ali Nuhu ya amsa tambayoyin da aka yi masa dangane da cire jarumar. Ya bayyana cewa yana da kwakkwaran dalilinsa na cire jarumar wanda hakan ne zai fi zama masa alkhairi, da jarumar da ma kamfanin gaba daya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe