27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Matsayin da na ba mahaifina na gida, shi na bai wa Adam Zango, Jaruma Tumba Gwaska

LabaraiKannywoodMatsayin da na ba mahaifina na gida, shi na bai wa Adam Zango, Jaruma Tumba Gwaska

Bayan wani gidan talabijin na FarinWata ya yi hira da jaruma Tumba Gwaska, an tambayeta akan yadda take da alaka mai karfi tsakaninta da Jarumi Adam A. Zango har wasu suke ganin kamar soyayya ce tsakaninsu, kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Sai dai a bayaninta, ta tabbatar da cewa babu soyayya tsakaninsu, Uban gidanta ne shi sannan matsayin uba yake a wurinta kuma akan shi sai inda karfinta ya kare.

Kamar yadda ta ce:

“To a gaskiya dai babu komai tsakanina da Baba Ado, Wallahi Wallahi babu komai tsakanina da Adamu sai mutunci. Yadda na dauki girma na ba mahaifina na gida, haka na dauka na ba Adam.

“Uban gidana ne shi, ina ji da shi, ina alfahari da shi kuma sai inda karfina ya kare akanshi saboda ai dan halak shi ake yi wa halacci inji bahaushe.”

Yayin da aka tabo ma Tumba batun Safara’u wanda tace musu ‘yan wahala, ta ce kowa yayi nagari don kansa.

Ta ce fim ne ya sanya Safara’u yin suna sannan babu yadda za ayi mutane su kalleta idan banda fim din da ya fito da ita.

Tumba ta ce korar Safara’u da aka yi daga fim shi ne ya bata mata rai har ta dauka zafi take caccakar sana’arsu.

Ummi Rahab: Adam A Zango ya saba auren yaran sa mata ni ba irin su ba ce

Bayan kura ta lafa a dambarwar dake tsakanin jarumi Adam A Zango da ‘yar dakin sa Ummi Rahab, a karon farko jarumar ta yi magana tun bayan fara dambarwar, inda a jiya ta samu tattaunawa da jaridar Daily Trust kan abin da ke tsakanin ta da Adam A Zango.

A cikin hirar Ummi Rahab ta bayyana cewa har yanzu tana daukar Adam A Zango a matsayin Uba, kuma tana girmama shi, amma kowa ya kama hanyar sa ba batun sake tafiya tare.

Haka zalika tayi karin haske kan cire ta da yayi daga cikin shirin “Farin Wata Sha Kallo”, inda ta bayyana yana da damar saka duk wanda ya so a fim din sa da cire duk wanda ya so ba ta da matsala da hakan, amma ta danganta hakan da kishin kula samarin da take, ya kuma yi kokarin hana ta taki hanuwa yasa shi yayi abinda yayi.

Ummi Rahab ta bayyana cewa ita baza ta iya auren shi ba tunda yana matsayin uba a wajenta, inda tace shi kuma ya gaza fahimtar hakan, ta ce ya saba da auren yaran sa mata da yake fim da su, sai dai ita ba haka take ba tana da ikon yin yadda ta so da rayuwar ta, indai tsarin bai sabawa shari’a ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe