27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tallafin da Aishatul Humaira ta ba wacce ta musulunta a TikTok ya janyo cece-kuce

LabaraiKannywoodTallafin da Aishatul Humaira ta ba wacce ta musulunta a TikTok ya janyo cece-kuce

Tashar Tsakar Gida ta bayyana yadda wata baiwar Allah ta musulunta a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok a makon da ya gabata ta hannun wani ma’abocin da’awa ta kafar, Abu Salma, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Ya yi bidiyo ne inda ya bayyana inda ta karbi kalmar shahadar da kuma irin taimakon da ta samu daga wurin mutane daban-daban wanda take bukata don ci gaba da addininta cikin salama.

Kamar yadda Abu Salma ya bayyana, yanzu haka an samu masu riketa har mutane biyu baya ga sauran tallafin da ta samu har Jaruma Aishatul Humaira ta Kannywood ta yi mata alkawarin sama mata aiki mai albashi mai tsoka kamar yadda Abu Salma ya karanta sakonta tare da yi mata godiya da fatan alkhairi.

Sai dai saboda caccakar da Abu Salma ya dade yana yi wa ‘yan fim akan cewa ko da sadaka suka yi da kudin fim Allah ba zai karba ba an yi caa akansa inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa.

Ganin caccakar da ya saba, da kuma yadda ya fito yana yaba wa Aisha tare da yi mata addu’o’i da fatan alkhairi ne ya janyo mutane suka dinga sukarsa.

Sai dai daga baya Abu Salma ya fito yayi bayani inda yace ko da arne ne ya baka kudi duk da baya da lada, idan kaci, ka ci halas balle kuma ita Humaira ba kudi ta bayar ba, aiki ne zata samar wa wannan wacce ta musulunta.

Fitacciyar ‘yar gwagwarmaya daga Tamil Nadu, Sabarimala ta Musulunta

Bayan karatun Qur’ani mai tsarki da tayi,Sabarimala Jayakanthan wata ‘yar kasar Indiya mai fafutukar kare hakkin bil’adama ta yi rabo ta musulunta. Sabarimala ta kasance sananniya ce a Kudancin Indiya.

Ta sami damar aikin umarah a watan Ramadan bana

Ta sami damar ziyartar kasar Saudiyya a wannan wata na Ramadan domin yin aikin Umrah saboda samun damar shiga musulunci da tayi. A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an hangeta tana karanta kalimatu Shahada yayin da take tsaye a cikin harabar masallacin Makkah.Yanzu haka ta chanza Sunanta zuwa Fatima Sabarimala.

Ta bayyana makasudin shigar ta musulunci

A wani faifan bidiyo, Sabrimala ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga musulunci. A cikin faifan bidiyon, an ji tana cewa “A Yanzu ina son Musulunci fiye da yadda nake son kaina.”
Sannan ta sake tambayan kanta dalilin da yasa ake nunawa al’ummar musulmi kiyayya , tare da rera karatun Al-Qur’ani cikin murya mai ban sha’awa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe