23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Bidiyo: Yadda aka titsiye wani dan sanda yana tsaka da busa tabar wiwi a wani kango

LabaraiBidiyo: Yadda aka titsiye wani dan sanda yana tsaka da busa tabar wiwi a wani kango

An kama wani dan sanda yana tsaka da busar tabar wiwi a wani kango wanda ya fi kama da gulbi sanye da kayan aikinsa, LIB ta ruwaito.

Hukumar ‘yan sandan kasar Ghana ta bayyana dan sandan a matsayin Sajan Isaac Sowah Nii na ofishin ‘yan sandan Accra.

Kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta saki takarda, yanzu haka ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a hukunta Sajan din bayan gurfanar da shi gaban kotu.

Ga bidiyon a kasa:

Gwamnatin jihar Kano ta titsiye mutumin da ya yi batanci ga Addinin Musulunci

A cikin irin makalolin da ake gabatarwa a wurin bikin Maulidi, a unguwar Ja’in dake garin Kano, wani magidanci mai suna Lawan Mundadu, yayi wani jawabi mai tattare da batanci ga addinin Musulunci.

Jawabin nasa ya ja hankalin hukumar kula da harkokin addinin Musulunci ta Jihar Kano inda hukumar ta titsiye shi domin jin bahasi daga gareshi.

A Jawabin da yayi, magidancin ya bayyana cewa wai Sharu Sani na Janbulo dake garin Kano, dashi akayi Isra’i da Mi’iraaji kuma dashi aka gana da Allah kuru-kuru.

Wannan jawabi da Lawan ya yi ya ruguntsuma tunanin kwamashinan hukumar, abin da ya gaggauta tisa keyar matashin zuwa gaban hukumar domin fuskantar tuhuma akan tabargazar.

Rahoton da Freedom Radio Kano ta ruwaito magidancin ya kuma bayyanawa cewa wai duk wanda baya kaunar Sharif Sani to tabbas dan wuta ne babu ko shakka a ciki.

A nasa jawabin yayin kare kai, Sharu Sani Janbulo, ya nesanta kansa daga wadancan kalamai na Lawan Mundadu, inda yace sam baya tare da wadancan kalamai. Hasalima shi baisan sanda akayi Isra’i da Mi’iraaji ba sai yanzu da yake karantawa a littafi. Inda kuma ya yayi tur da Allah wadai da wadancan miyagun kalamai.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe