28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Hotunan wasu ‘yan mata 2 yayin da suke ba hammata iska akan saurayi

LabaraiHotunan wasu 'yan mata 2 yayin da suke ba hammata iska akan saurayi

An dauki hotunan wasu ‘yan mata biyu masu karancin shekaru yayin da suke tsaka goge raini ta hanyar kwasar dambe akan wani saurayi, LIB ta ruwaito.

An hango wasu ‘yan mata biyu masu karancin shekaru yayin da suke tsaka da kwasar dambe akan namiji.

Lamarin ya faru ne a Limbe, yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Wasu ma’abota amfani da kafar Facebook ne su ka wallafa hotunan a ranar Juma’a, 10 ga watan Yuni.

Sun bayyana cewa mata da dama suna ci gaba da dambe akan maza a yankin.

Kamar yadda wani Clement Toh da ya wallafa ya ce:

“‘Yan matan Limbe ba za su dena tozarta kansu ba ta hanyar gasar dambe akan maza ba. Lallai sun dauki maza da matukar muhimmanci.”

Ana tsaka da shagalin sallah, wasu kawaye biyu sun ba hammata iska akan saurayi a Jihar Neja

A ranar Litinin, 2 ga watan Mayu wasu ‘yan mata biyu a Minna da ke Jihar Neja sun kwashi damben nushi akan wani saurayi.

An samu bayani akan yadda kawayen juna guda biyu su ka bar shagalin sallah inda suka dinga dambe bayan gano cewa da saurayi daya su biyun su ke soyayya.

A bidiyon an ga yadda duk su ka cire dankwalayensu da mayafai su ka dinga dauki ba dadi yayin da sauran kawaye su ka zuba musu na mujiya.

Lamarin ya bai wa mutane da dama mamaki yayin da wasu su ke ganin hakan shirme ne don dakyar idan saurayin ya san su na yi.

Shafin Instablog9ja ya wallafa guntun bidiyon wanda da alamu kamar a wurin kwalliya aka dauke shi don an rubuta Girbiza’s Touch a wurin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe