23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Dalilan da su ka sanya Ganduje yafi cancanta da zama mataimakin Tinubu a APC -Hadimin gwamna

LabaraiDalilan da su ka sanya Ganduje yafi cancanta da zama mataimakin Tinubu a APC -Hadimin gwamna

A yayin da ake tsaka da neman shawarwari kan wanda zai zama mataimakin shigaban ƙasa ga ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wani mai taimakawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kan harkokin sadarwa, Shehu Isa, ya kawo dalilan da su ka sanya Ganduje yafi dacewa APC da Tinubu su ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Isa wanda yayi ƙarin haske kan takarar musulmi da musulmi, inda yake cewa ba sji a cikin kundin tsarin mulki, yayi nuni da cewa Ganduje shine yafi cancanta da zama mataimakin Tinubu a ƙarƙashin jam’iyyar. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya kawo dalilan da su ka sanya APC da Tinubu yakamata su ɗauki Ganduje a matsayin mataimaki

Mai taimakawa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ‘yan jarida a ƙarshen mako a birnin Kano.

A cewar sa:

ldan akayi duba da ƙwarewa da nasarori a fannin aikin gwamnati da siyasa, sannan da irin halayen sa, Ganduje ne kaɗai zaɓin da APC take da shi

Ganduje ne kaɗai a Arewa ya tsaya kai da fata wajen yaƙin neman zaɓen Tinubu, duk da ƙalubalen da ke ciki da yadda wasu manyan ƙusoshin a Arewa su ke tsoron mara masa baya a bayyane.

Ba ya da ƙabilanci, duk da cewa ɗan Fulani ne, ya aurar da ɗiyar sa ga Bayerabe. Hatta Tinubu zai samu natsuwar aiki da shi a matsayin mataimaki.

A matsayin mataimaki, Ganduje zai sa baki akan rikicin Fulani, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran ayyukan laifuka dake addabar ƙasar nan a matsayin sa na cikakken ɗan Fulanin asali.

Yayi ƙarin haske kan takarar musulmi da musulmi

Dangane da ƙalubalen dake tattare da takarar musulmi da musulmi, Isa yace:

Ba hakan a cikin kundin tsarin mulki sannan jihar Kaduna ta jaraba yin hakan, kuma tun faruwar hakan jihar ta samu zaman lafiya inda rikicin ƙabilanci ya ƙaurace mata wanda tayi ƙaurin suna akai.

Kwararan ‘yan siyasa guda  uku 3 na Arewa  wadanda ake hasashen Tunibu zai iya daukar dayan su mataimaki

A wani labari kuma na daban mun kawo muku jerin manyan ‘yan siyasa guda uku 3 na Arewa  wadanda ake hasashen Tunibu zai iya daukar dayan su mataimaki.

Yayin da kakar zaben shugaban kasa ke karatowa a shekarar 2023, yan siyasa a jamiyyar APC mai mulki, na ci gaba da neman takarar mataimakin shugaban kasa, bayan kammala zaben fidda gwani na da jamiyyar ta gudanar, wanda Asiwaju Bola Ahmad Tunibu ya yi nasarar zama dan takarar, gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2023. 

Bola Ahmad Tunibu, wanda ya fito daga yankin kudu maso yamma na Najeriya, zai dauki mataimakin sa ne daga Arewa a zaben na shekarar 2023, domin fatan samun kuri’u masu yawa daga Arewacin Najeriya, saboda gaskiyar cewa, Arewacin Najeriya tana da ruwa da tsaki wajen yanke waye zai zama shugaban kasar Nageriya na gaba

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe