24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Kotu ta tura wasu gardawa biyu gidan gyaran hali bisa ɗirkawa yarinya ‘yar shekara 13 fyaɗe

LabaraiKotu ta tura wasu gardawa biyu gidan gyaran hali bisa ɗirkawa yarinya 'yar shekara 13 fyaɗe

Wata kotun majistare ta Ikeja a jihar Legas ta tura wasu mutum biyu masu suna Sakiru Oladosu, mai shekaru 50, da Tola Rasaq, mai shekaru 40, gidan gyaran hali bisa laifin yin fyaɗe da ɗirkawa wata yarinya mai shekaru 13 a duniya ciki.

Mutum biyun da ake zargi waɗanda kuma su ka kai yarinyar wajen zubar da ciki bayan sun yi mata wannan ɗanyen aikin, suna rayuwa ne a yankin Mushin cikin Legas.

Ana tuhumar su da laifin yin fyaɗe da yunƙurin zubar da ciki

Shafin LIB ya rahoto cewa ana tuhumar su da laifin yin fyaɗe da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba waɗanda ke da hukuncin ɗaurin rai da rai da kuma shekara uku a gidan kaso a ƙarƙashin dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.

Da yake jawabi ga kotun, mai shigar da ƙara, DSP Kehinde Ajayi, yace waɗanda ake tuhumar sun aikata laifukan cikin watan Fabrairu a titin Odusanmi, Mushin a jihar Legas. Oladosu ya yaudari yarinyar zuwa gidan sa, inda yayi mata fyaɗe sannan ya ɗirka mata ciki.

Ajayi yace:

Wanda ake ƙarar ya kai yarinyar zuwa wani shagon sayar da magani a titin Ashofin, a yankin Okareju Mushin na jihar Legas.

Oladasu ya haɗa baki da Rasaq wajen biyan N4,000 domin yi wa yarinyar allurar zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba.

An tura su gidan gyaran hali

Mai shari’a Kubeinje bai saurari roƙon da waɗanda ake zargin su kayi ba, inda ya umurci da a sakaya su a gidan gyaran hali na Kirikiri.

An ɗage sauraron ƙarar har zuwa 7 ga watan Yulin 2022.

Daga zuwa yayi mata addu’a fasto yayi wa yarinya ‘yar shekara 13 fyaɗe

A wani labari na daban kuma, wani fasto yayi fyaɗe ga yarinya ‘yar shekara 13 a duniya.

Wata babbar kotu a birnin Uyo, wacce mai shari’a, Bassey Nkanang, ke jagoranta ta tura wani fasto, Godson Thompson, mai shekaru 32 gidan kaso bisa zargin yin fyaɗe ga wata yarinya ‘yar shekara 13, wacce aka kawo wajen sa yayi mata addu’a.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa, alƙali Nkanang ya bada umurnin a tsare faston da ake zargin, wanda ɗan asalin garin Ikot Offiong Nsit cikin ƙaramar hukumar Nsit Ibom ta jihar Akwa Ibom, bayan ya saurari shedun da yarinyar ta kawo wacce ɗalibar makarantar sakandire ce.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe