22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Mawaki Justin Bieber yana fama da cutar shanyewar barin fuska

LabaraiMawaki Justin Bieber yana fama da cutar shanyewar barin fuska

Mawakin kasar Canada, Justin Beiber ya bayyana yadda yake fama da cutar shanyewar barin fuska.

Mawakin ya sanar da hakan ne ta shafinsa na Instagram ranar Juma’a, 10 ga watan Yunin 2022.

Kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo:

“Ina son sanar da ku abinda ya ke faruwa ne. Idan kun kula da fuskata, ina fama da wata cuta mai suna “Ramsay Hunt Syndrome” kuma ta taba jijita ta kunne da kuma fuska, hakan yasa barin fuskata daya ya shanye.

“Idan kun kula, bana iya kifta idona daya kuma ba na iya murmushi ta bangaren. Har hancina ma baya motsi ta bangaren. Gaba daya ya gefen ya shanye.

“Game da wadanda suka fusata akan yadda na fasa wasanni, su kula da cewa lafiya ta ce ta janyo hakan. Wannan abin ya fara tsananta. Naso ace hakan bai faru ba, amma ya kamata in dakata don tabbatar da lafiyar jikina.”

Ga bidiyon a kasa:

Cutar Ramsay Hunt Syndrome tana da matukar zafi kusa da kunne, fuska da kuma baki.

Yana faruwa ne idan wata kwayar cuta ta sami wata jijiya da ke fuskar mutum. Kuma ba wannan bane karon farko da wata cuta ta samu mawakin ba.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2020, mawakin ya yi fama da cutar Lyme. Kuma a lokacin ya yi wata wallafa kamar haka:

“Yayin da mutane suke ta sukar sauyawar kamannin Justin Bieber, sun kasa gane cewa ina fama da cutar Lyme kuma ta taba fata ta, aikin kwakwalwa ta, karfina da gaba daya lafiyata.”

Muna masa fatan waraka.

MashaAllah: Matar Jarumin kannywood kuma mawaki Garzali miko ta haihu

A yammacin ranar Talata Jarumi kuma mawakin Kannywood, Garzali miko ya wallafa batun samun karuwar da ya yi a shafinsa na Instagram.

Kamar yadda ya bayyana, Allah ya azurta shi da haihuwar da namiji. Ya kuma wallafa hotunansa rungume da sabon jaririn.

Kamar yadda ya rubuta:

“Alhamdulillah, Allah ya azurtani da da namiji yau 7 ga watan Yunin shekarar 2022.

“Allah abin godiya, Allah yasa ka zo duniya a sa’a. Allah ya amfani rayuwarka.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe