23 C
Abuja
Sunday, September 25, 2022

Kwararan ‘yan siyasa guda  uku 3 na Arewa  wadanda ake hasashen Tunibu zai iya daukar dayan su mataimaki 

LabaraiKwararan 'yan siyasa guda  uku 3 na Arewa  wadanda ake hasashen Tunibu zai iya daukar dayan su mataimaki 

Yayin da kakar zaben shugaban kasa ke karatowa a shekarar 2023, yan siyasa a jamiyyar APC mai mulki, na ci gaba da neman takarar mataimakin shugaban kasa, bayan kammala zaben fidda gwani na da jamiyyar ta gudanar, wanda Asiwaju Bola Ahmad Tunibu ya yi nasarar zama dan takarar, gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2023. 

Bola Ahmad Tunibun, wanda ya fito daga yankin kudu maso yamma na Najeriya, zai dauki mataimakin sa ne daga Arewa a zaben na shekarar 2023, domin fatan samun kuri’u masu yawa daga Arewacin Najeriya, saboda gaskiyar cewa, Arewacin Najeriya din tana da ruwa da tsaki wajen yanke waye zai zama shugaban kasar Nageriya na gaba. 

1. Umar Ganduje 

IMG 20220609 192730
Dr. Abduiiahi Umar Ganduje gwamnan jihar Kano

Mutum na farko shine, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda shine gwamnan jihar Kano wanda zai sauka, kuma yana daga cikin shugabanni masu fada a ji na jamiyyar ta APC, a Arewacin Najeriya. 

Za’a iya saka masa da gurbin mataimakin shugaban kasa, sabida nuna goyon bayan sa ga muradin takarar Tunibun, domin samun kuri’u masu yawa a jihar ta Kano. 

2.  Kashim Shettima

IMG 20220609 192549
Kashim Shettima tsohon gwamnan jihar Borno

Kashim Shettima, shine tsohon gwamnan jihar Borno, kuma shakikin aboki ne ga shi Asiwaju Bola Ahmad Tunibu din. 

Dan takarar Shugabancin kasar zai iya daukar sa a matsayin mataimakin sa a zaben na shekarar 2023.

3. Yahaya Bello

IMG 20220609 192646
Yahaya Bello gwamnan jihar Kogi

Yahaya Bello, shine gwamnan jihar Kogi mai ci a halin yanzu, yana da karfi a jamiyyar APC, kuma yana da matukar tasiri a siyasar arewacin Najeriya. 

Yana daya daga cikin yan takarar Shugabancin kasa da suka kara da shi Bola Ahmad Tunibun. Jamiyya mai ci ta APC din za ta iya bashi gurbin mataimakin shugaban kasa, domin  a lallashe shi.

“Ni matashi ne mai jini a jika”, Tinubu

Bidiyon Tinubu wanda ya ke shaida wa magoya bayan sa yayin ci gaba da yawon neman amincewa da shi domin zama shugaban ƙasa ya yadu a kafafen sada zumunta, LIB ta ruwaito.

Ɗan takarar shugabancin ƙasa kuma jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shi matashi ne kuma yana da kuzarin da zai iya shugabancin Najeriya.

Tsohon gwamnan Jihar Legas ɗin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu ƴan jam’iyyar APC tare da magoya bayan sa a ƙarshen mako.

Tinubu ya ce APC zata ci gaba da kare muradin ƴan Najeriyan da ke zaune a ciki da wajen ƙasar nan tare da tabbatar da cewa ƙasar ta kasance abisa tafarkin da ya dace.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe