23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wata mata ‘yar Najeriya ta mayar da N14.9m da ta tsinta, an bata kyautar maƙudan kuɗaɗe

LabaraiWata mata 'yar Najeriya ta mayar da N14.9m da ta tsinta, an bata kyautar maƙudan kuɗaɗe

Wata mata ‘yar Najeriya mai suna Vicky Umodu, wacce ke rayuwa a San Bernardino California, ta nuna tsantsar gaskiya bayan ta mayar da zunzurutun kuɗi har N14.9m, wanda ta tsinta a cikin kujera. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

An kawo mata kujerun har gida

Wasu mutane masu son bayar da kujerun kyauta ne su ka kawo wa Umodu kujerun har gida.

Matar dai ta tare ne a cikin sabon gidan ta dake a California, inda take neman sababbin kayan ɗaki na siya a shafin Craigslists.

Ta samu cewa akwai wasu mutane dake son yin kyautar kayan ɗakin wani ɗan’uwan su da ya rasu. Sai kawai ta nemi da a kawo mata su. Bayan an kawo mata kujerun, yayin da take duba su, sai kawai taga maƙudan kuɗaɗe ajiye a ɗaya daga cikin su.

Matar ta bayyana yadda lamarin ya auku

Umodu ta bayyana cewa:

Ban daɗe da tarewa ba, sannan bani da komai a cikin gidan. Naji daɗi sosai, sai mu ka ɗauko su zuwa cikin gidan.

Ina cewa yaro na, zo nan zo nan, wannan kuɗi ne! dole na kira mutumin!

Sun nemi mutanen da su ka basu kujerun inda su ka mayar musu da kuɗaɗen.

Umodu tace:

Ubangiji yayi min komai ni da yara na. Suna raye cikin ƙoshin lafiya. Ina da jikoki gida uku, me kuma zan nemi a wajen ubangiji?

Bayan ta mayar da kuɗin, an bata kyautar N900,000 saboda gaskiyar ta.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

lulusmooth ya rubuta:

Ni gaskiya sai na ajiye su kamar na shekara ɗaya a wuri na kafin na mayar da su.

@poshest_hope ya rubuta:

Haka yakamata. Ba kuɗin ta bane.

@gucci_tos ya rubuta:

Ta yaya za su ajiye makuɗan kuɗaɗen idan ba shiri bane.

Wani matukin keke Napep ya dawo da jaka mai dauke da wayoyin hannu 10 ga mai su, bayan ya mantasu a bin hawansa inda aka bashi N1000 ladan tsuntuwa

A wani labari na daban kuma, matuƙin keke Napep ya mayar da kayan da aka manta da su a keken sa, an bashi ladan tsintuwa.

Halayyar gaskiya da wani matukin keke napep ya nuna ya taba zukata a yanar gizo, inda aka mai dashi abin yabo. 

Matukin dan Najeriya, ya gano cewa wani fasinja, ya manta wata jakarsa a cikin abin hawansa, wadda take dauke da wayoyi sababbi har guda goma, inda shi kuma ya dauki aniyar zakulo mai kayan. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe