23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Tsohon bidiyon Fasto Tunde Bakare yana ce wa mambobin cocinsa Ubangiji ya nuna masa zai maye gurbin Buhari a 2023

LabaraiTsohon bidiyon Fasto Tunde Bakare yana ce wa mambobin cocinsa Ubangiji ya nuna masa zai maye gurbin Buhari a 2023

An samu tsohon bidiyon Fasto Tunde Bakare yana sanar da mambobin cocinsa cewa shi ne zai dar kujerar shugabancin Najeriya bayan Buhari, LIB ta ruwaito.

Yayin da ya ke wa’azi a cocin a ranar, faston ya kada baki ya ce:

“Ku fada a duk inda ku ke son fadi. Idan kun taba ji a wani wuri, ina maimaita muku cewa in dai a siyasar Najeriya ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne shugaban kasar nan na 15, ni ne zan zama na 16.

“Ban taba fada muku ba a baya. Amma a yau na bayyana muku, da safiyar nan ina sanar da ku cewa babu abinda zai sauya wannan maganar da yardar Jesus.”

Fasto Bakare ya biya N100m na kudin fom din takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC amma bai samu kuri’a ko guda daya ba a wannan zaben fida da gwanin da aka gama.

Ga bidiyon a kasa:

Yadda fasto ya yi layar zana da mambobin coci fiye da 20

Har yanzu dai ba a san inda Fasto Kalibala Samuel da mambobin cocinsa 20 su je ba kudanmako daya kenan, Legit.ng ta ruwaito.

Sai da Kalibala ya yi musu huduba mai ratsa jiki wacce ta sa su ka amince inda su ka rufe gidajensu su ka bi shi wani muri tare da kulle wayoyinsa.

Tuni ‘yan sandan yankin Mityana da ke kasar Uganda su ka bazama su na ta nemansu bayan batarsu inda ake fatan za a nemosu su dawo ga ‘yan uwansu.

An nemi wayoyinsu amma duk a kashe su ke kamar yadda ‘yan sandan su ka tabbatar. Kuma cikin mambobin gidaje bakwai da ya yi layar zanar da su akwai Namuwaya Jesca, Ssekyewa Shakim mai shekaru 19, Nampeewo Shifrah mai shekaru 17, Muteesasira Muhammad mai shekaru 10, Ssenabulya Muhammed mai shekaru 8, Nakintu Angel mai shekaru 4 da kuma Uwuzeeye Mable.

Bayanai sun nuna cewa sai da faston da mabiyan nasa sun rufe gidajensu ne sannan sun kashe wayoyinsu.

Kamar yadda takardar ‘yan sanda ta nuna, akwai mutum daya da ya samu yin magana da diyarsa wacce ba a riga an wuce da ita ba. Sai dai su na gama magana ta kashe wayarta ba tare da ya san inda ta ke ba.

‘Yan sandan Uganda sun yi alkawarin bin sawunsu

Rundunar ‘yan sandan Uganda ta yi alawadai da wannan mummunan lamari da faston ya yi, inda ta kara da cewa ya yi amfani da wata dabara ne wurin tafiya da mabiyan nasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe