23 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Zaɓen fidda gwanin APC: ‘Yan takara 9 da su ka janye da wanda su ka marawa baya

LabaraiZaɓen fidda gwanin APC: 'Yan takara 9 da su ka janye da wanda su ka marawa baya

Abin da yafi ɗaukar hankali a wurin babban taron APC na ƙasa domin zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa, shine yadda ‘yan takara da dama su ka janye daga yin takara.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, a lokacin da aka fara taron da yammacin ranar Talata, akwai ‘yan takara 23 masu neman kujerar. Amma bayan kowanne daga cikin su ya gabatar da kan sa, ‘yan takara 14 ne kawai su ka rage daga cikin fafatawar neman takarar domin zama ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar.

‘Yan takara da dama sun janye wa Tinubu

Bakwai daga cikin ‘yan takarar sun janye wa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, sannan su ka mara masa baya.

Sai dai wani ɗan takara ɗaya, ya janye wa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Tun da farko, Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya janye daga yin takara kafin a fara taron. Amma sai dai ba kamar sauran ‘yan takarar da su ka janye ba, Nnamani bai nuna goyon bayan kowa ba daga cikin ‘yan takarar.

Waɗanda su ka janye daga yin takara da kuma wanda su ka marawa baya

Ga sunayen ‘yan takara 9 da su ks janye da kuma wanda su ka marawa baya:

1. Gwamnan jihar, Abubakar Badaru, ya janye wa Bola Tinubu.

2. Tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Dimeji Bankole, ya janye wa Bola Tinubu.

3. Sanata mai wakiltar Ondo ta Arewa, Ajayi Boroffice, ya janye wa Bola Tinubu.

4. Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya janye wa Bola Tinubu.

5. Tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio, ya janye wa  Bola Tinubu.

6. Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan jihar Ogun, ya janye wa Bola Tinubu.

7. Uju-Kennedy Ohanenye, ‘yar takara mace ɗaya tilo, ta janye wa Bola Tinubu.

8. Nicholas Felix, ya janye wa mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo.

9. Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, ya janye ne kawai daga takara ba tare da bayyana wanda yake marawa baya ba daga cikin sauran ‘yan takarar.

Jimillar deliget 2,203 daga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja ne, aka tantance dai domin gudanar da zaɓen.

Kwamitin tantance ‘yan takarar APC, ya kori 10 daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa

Kwamitin tantance ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kori ‘yan takara 10 daga cikin waɗanda za su fafata a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar wanda zai gudana a sati mai zuwa.

Shugaban kwamitin, John Oyegun, ya bayyana hakan a ranar Juma’a. A cewar rahoton Channels Tv

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe