22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Jami’an DSS sun kubutar da mahaifiyar AA Zaura a jihar Jigawa 

LabaraiJami'an DSS sun kubutar da mahaifiyar AA Zaura a jihar Jigawa 

Awa 24 kenan bayan  sace Hajiya Laure Mai Kunu, mahaifiya ga dan takarar sanata na Kano ta tsakiya, A’A Zaura, gami da yin garkuwa da ita, ma’aikata masu aiki a bangaren DSS wato (Department of State Service) a ranar Talata, a can surkukin jihar Jigawa. 

mahaifiya
Jami’an DSS sun kubutar da mahaifiyar AA Zaura a jihar Jigawa 

Yan bindigar sun dauke mahaifiyar AA Zaura din ne ita kadai

Yan bindiga da ba’a san adadin su ba, sun yi wa garin Zaura dake karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano tsinke, inda suka yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar sanata na jamiyyar APC, a ranar Litinin. 

Shugaban karamar hukumar Ungogo Abdullahi Ramat, shine ya tabbatar wa da wakilin jaridar Punch, cewa an kubutar da ita a ranar Litinin, a jihar Jigawa. 

An kubutar da ita tare da wasu dattijai

Haka kuma, wani babban jami’i na sashen DSS din, wanda yaki yarda a buga sunan sa, ya ce, sun kubutar da Laure din, mahaifiya ga AA Zauran ne, tare da wadansu tsofaffi wadanda aka yi garkuwa da su, kimanin kwanaki 10 da suka gabata.

An harbe ‘yan garkuwa da mutane guda 3 an kubutar da mutane a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta sanar da bindige yan garkuwa da mutane guda uku, tare da kubutar da mutane biyu da aka sace , a kauyen Katsinawa dake karamar hukumar Tudun Wada dake jihar. 


Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa, yace jami’an sun sami bindiga kirar AK47 ta gida, da kuma alburusai guda shida. Sannan wasu fusatattun yan sanda, sun kone wani daga cikin masu garkuwar a lokacin artabu. 

Yadda labarin yan garkuwar ya ishe ‘yan sandan


Da yake kara bayani, Kiyawan yace, sun sami  labarin ne da misalin karfe 0130hrs, alissafin jami’an tsaro, wato karfe, 1:30 na dare kenan, cewa yan bindiga sun yiwa gidan wani Elisha Aminu dake kauyen Katsinawa a karamar hukumar Tudun Wada, inda suka sace yayan sa mata guda biyu,  Zainab Elisha, yar shekara 18, da kuma Nafisa Elisha, yar shekara 16, sannan sun gudu dajin Falgore.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe