24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin bam ɗin da aka kai a cocin Katolika ta jihar Ondo

LabaraiShugaba Buhari yayi Allah wadai da harin bam ɗin da aka kai a cocin Katolika ta jihar Ondo

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin bam ɗin da aka kai a cocin katolika ta jihar Ondo. Harin ya auku ne ranar Lahadi a cocin St Francis Catholic Church, dake a titin Owa-luwa, kusa da fadar Olowo na Owo a jihar Ondo.

An buɗe wa masu bauta wuta a harin

Harin ya auku ne bayan da wasu da ake tunanin ‘yan ta’adda ne su ka tayar da bam a cikin cocin sannan su ka ɓude ma masu bauta wuta.

Mutane da dama sun rasa rayukan su, yayin da wasu su ka samu raunika, ƙananan yara na daga cikin waɗanda su ka ransu a harin.

Shugaba Buhari ya aike da saƙon ta’aziyyar sa

A wani sako da shugaba Buhari ya fitar a shafin Twitter, ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda abin ya ritsa da su, cocin katolika da kuma gwamnatin jihar Ondo.

Shugaba Buhari kuma ya umurci hukumomin bayar da agajin gaggawa da su gaggauta ceto rayukan waɗanda su ka samu raunika.

Duk rintsi, ɓata gari da muggan mutane ba zasu taɓa nasara akan ƙasar nan ba, duhu ba zai taɓa dusashe haske ba. Najeriya za tayi nasara.

A cewar shugaba Buhari

Buhari ya gana da waɗanda bam ya tashi da su a Kano, ya nuna matuƙar jimamin sa

A wani labari na daban kuma Shugaba Buhari ya gana da waɗanda bam ya tashi da su a jihar Kano. Shugaban ƙasar ya kuma nuna matuƙar alhinin sa akan lamarin.

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi da su a jihar Kano, domin yi mu su gaisuwa da yawun yan kasa baki daya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa shuugaban ƙasar ya bayyana lamarin, wanda mutane a kalla tara 9 suka mutu, 22 kuma su ka jikkata suke karbar kulawa a asibiti, da cewa abin baƙin ciki ne kuma abin takaici.

Babban mai taimakawa shugaban kasar ta fannin kafar yada labarai, Malam Garba Shehu, shine ya tabbatar da ganawar shugaban kasar da iyalan waɗanda abin ya shafa a ranar Litinin a Abuja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe