27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kano: Mutane 120 na kwance a gadon asibiti bayan shakar gurbataccen sinadarin gas a iska

LabaraiKano: Mutane 120 na kwance a gadon asibiti bayan shakar gurbataccen sinadarin gas a iska

Fiye da mutane 120, yawanci mata da yara, su na kwance a gadon asibiti bisa zargin iskar gurbataccen gas ta watsu kusa da Mundadu da ke cikin garin Kano a ranar Juma’a, 3 ga watan Yuni, LIB ta ruwaito.

Dailytrust ta ruwaito cewa mazauna yankin sun bayyana yadda wani Saifullahi dan jari bola garin tara karafa ya fasa karfen da sinadarin gas din ya ke ciki.

Shugaban gundumar, Magaji Abdullahi yayin bayani akan lamarin, ya kada baki ya ce:

“An sanar da ni da yamman nan cewa akwai matsala a wurin aikin jari bolar Saifullahi.”

Yayin tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’an hukumar kwana-kwanan Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya ce an garzaya da mutane da dama zuwa asibiti don a duba lafiyarsu.

A cewarsa:

“Kusan mutane 70 su na asibitin Jaen yayin da mutane 50 ke asibitin kwararru na Murtala Muhammad ana kulawa da lafiyarsu.”

Ya ce har yanzu dai babu wanda ya rasa ransa.

Matar aure ta haihu a bandakin asibiti, ba ta taba sanin tana da juna biyu ba

Wata matar aure bata taɓa sanin tana ɗauke da juna biyu ba har sai lokacin da ta ga hannun jaririn ta a cikin robar ɓandaki yayin da take ƙoƙarin ƙwarara ruwa bayan ta gama amfani da shi. Shafin LIB ya ruwaito

Lalene Malik, mai shekaru 23, ‘yan’uwan ta sun garzaya da ita zuwa asibitin A&E a Northwick Park Hospital, cikin Harrow, birnin Landan, bayan tayi ƙorafin tana fama da matsanancin ciwon ciki a gidan ta dake a Greenford, west London, ranar 26 ga watan Maris.

Ta sha magungunan hana ɗaukar juna biyu

Ta bayyana cewa tana shan magungunan hana ɗaukar ciki, sannan kuma tayi gwajin juna biyu har sau biyu a watan Fabrairun 2022 inda su ka nuna bata ɗauke da juna biyu.

Saboda haka kawai sai ta ɗauka cewa ciwon cikin na ta ɓacin ciki ne kawai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe