28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

‘Yar uwata ta hana ni shiga cikin kawayenta da bikinta saboda na cika kiba

Labarai‘Yar uwata ta hana ni shiga cikin kawayenta da bikinta saboda na cika kiba

Wata ‘yar Najeriya ta bayyana dalilinta na fasa zuwa auren ‘yar uwarta saboda ta ce ba za ta shiga cikin jerin kawayenta ba don kiba ta yi mata yawa, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda matashiyar mai suna Zioraife ta wallafa ta Twitter, ta ce ‘yan uwanta su na yawan zundenta akan kibarta.

Kamar yadda ta wallafa ranar 5 ga watan Yuni:

“Yar uwata da mu ka fi kusanci ta tabbatar min da cewa ba zan shiga jerin kawayenta ba saboda na cika ki a. Sai dai ko in rage kiba kafin watan Disamba ko kuma in hakura. Ba zan je bikinta ba.”

“Yan uwana ba su da kirki, su na yi min wulakanci. Gara in tsaya a gida inta latsa wayata. Ina miki fatan alkhairi.

“Wadannan ne wadanca ya dace su dinga ba ni kwarin gwiwa akan jikina, amma su na min wulakanci. Duk lokacin da na ke cin abinci sai su dinga korafi akan yawan cin abinci na.”

Ana tsaka da shagalin sallah, wasu kawaye biyu sun ba hammata iska akan saurayi a Jihar Neja

A ranar Litinin, 2 ga watan Mayu wasu ‘yan mata biyu a Minna da ke Jihar Neja sun kwashi damben nushi akan wani saurayi.

An samu bayani akan yadda kawayen juna guda biyu su ka bar shagalin sallah inda suka dinga dambe bayan gano cewa da saurayi daya su biyun su ke soyayya.

A bidiyon an ga yadda duk su ka cire dankwalayensu da mayafai su ka dinga dauki ba dadi yayin da sauran kawaye su ka zuba musu na mujiya.

Lamarin ya bai wa mutane da dama mamaki yayin da wasu su ke ganin hakan shirme ne don dakyar idan saurayin ya san su na yi.

Shafin Instablog9ja ya wallafa guntun bidiyon wanda da alamu kamar a wurin kwalliya aka dauke shi don an rubuta Girbiza’s Touch a wurin.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe