22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Bayan zaman dadiron shekaru 11 da haihuwar yara 2, mawakiya Shakira da saurayinta sun rabu

LabaraiBayan zaman dadiron shekaru 11 da haihuwar yara 2, mawakiya Shakira da saurayinta sun rabu

Mawakiyar kasar Kolombiya, mai shekaru 45, Shakira da saurayinta, Gerard Piqué, mai shekaru 35 sun rabu bayan shekaru 11 da su ke tarraya tare da haihuwar yara biyu, Daily Mail ta ruwaito.

shakira and pique
Bayan zaman dadiron shekaru 11 da haihuwar yara 2, mawakiya Shakira da saurayinta sun rabu

Kamar yadda ta saki wata takarda:

“Muna bakin cikin sanar da ku cewa zamu rabu. Saboda farin cikin yaranmu wanda shi ne abu mafi muhimmanci, muna fatan za ku girmama hakan.

“Mun gode da fahimtarku.”

A shekarar 2017 aka dinga yada labarin rabuwar masoyan inda aka ce sun dena zama tare. Inda Shakira ta bayyana rashin jituwar da ke tsakaninsu a wata waka da ta saki.

Kamar yadda ta saki wasu baituka:

“Wurin kokarin cikasa ka, ta farfashe; na ja kunnenka amma ba ka ji ba; sai daga baya na fahimci karya ka ke yi….”

Tun shekarar 2011 masoyan su ke tare, sun hadu ne yayin da ta ke shirya bidiyon wata wakar da ta fi ta gasar kofin kwallon duniya mai suna Waka Waka.

Ta bayyana batun rabuwarsu

Mawakiyar mai shekaru 45 ta tabbatar da rabuwarsu yayin da ake tsaka da yada labarai akan cewa ya ha’inceta da wata.

Jaridar Spain ta El Pariodico ta ruwaito cewa sun raba gari ne bayan makwanni kadan da mawakiyar ta fatattaki Pique.

Majiyoyi sun bayyana yadda Pique ya koma sharholiyarsa yana rayuwa irin ta tuzurai tare da kwana da abokan harkarsa.

Na ga fa’i’doji da dama na zaman dadiron da na yi da mata ta kafin aure, Jarumi Ibrahim Suleiman

Jarumin fina-finan kudancin Najeriya, Nollywood, Ibrahim Suleiman ya bayyana fa’idojin da ya samu sakamakon zaman dadiron da ya yi da matar sa kafin aure.

Kamar yadda Suleiman ya yi tsokaci karkashin wallafar wata Ebelechukwu a shafin ta na Twitter, kamar yadda shafin Instablog na Facebook ya wallafa, ya ce akwai fahimtar juna sosai da suka samu sakamakon ‘yan makwannin da suka yi da juna shi da matarsa ba tare da aure ba.

Kamar yadda ta yi wallafar:

“Wannan tunatarwa ce, a matsayin ka na kirista, ba daidai bane ka yi zaman dadiro da mata kafin ka aure ta ba.”

Ibrahim Suleiman ya je karkashin wallafar inda yace:

“Gaskiya ne. Amma hakan na daya daga cikin abubuwan da basu dace ba da na ji dadin aikatawa duk da dai na ‘yan makwanni ne.

“Zaman ya yi min dadi kuma na ga fa’idar yin hakan.

“Da dadi ku samu damar dubi ga fuskokin junayen ku ko yaushe, dare da rana. Yana da kyau ku fahimci juna dakyau.

“Yanzu zan iya fadin abubuwa da dama dangane da mata ta. Ni fa bana karya, kullum buri na in kara inganta rayuwa ta. Amma ko da sau daya ne, ya kamata ka amsa wani laifin da ka taba aikatawa.”

Wallafar tasa ta dauki hankali kwarai, inda mutane da dama suka dinga sukar sa, wasu kuma suke yaba masa akan bayyana gaskiyar da ya yi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe