27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Yadda matasa su ka lakada wa barawon janarato duka sannan su ka yi masa tumbir

LabaraiYadda matasa su ka lakada wa barawon janarato duka sannan su ka yi masa tumbir

Wani dan jari bola ya ci bakin duka a hannun jama’a bisa zarginsa da satar janarato guda uku a Bayelsa, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda wasu ma’abota amfani da kafar Facebook su ka wallafa hotuna, lamarin ya auku ne a ranar 1 ga watan Yuni a Yenagoa, babban birnin jihar.

Ya yi satar ne a Boropit da ke kan titin NIIT, Etegwe Yenagoa. Mutumin ma’aboci jari bola ne kuma sun kusa halaka shi bayan kama shi da satar janarato guda uku kamar yadda wani ganau ya shaida.

Ga hotunan a kasa:

theif
Yadda matasa su ka lakada wa barawon janarato duka sannan su ka yi masa tumbir
beating

Yadda wasu matasa suka tasa wa barawo taliya, bayan ya lamushe suka hau jibgarsa

An ba wa wani da ake zargin barawon kebur ne kwanon taliya, yayin da ake mishi horo a yankin Agorogbene na karamar hukumar Sagbama dake jihar Bayelsa, LIB ta ruwaito.

An kama wanda ake zargin, Preye Ayase da abokin harkarsa, Ringo Tareladei dumu-dumu suna satar keburan wutar da ke sada Ogobiri da yankin Agorogbene cikin Sagbama a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu.

Sai dai, Oiseibai Seperegha Godsgift M, shugaban kungiyar matasan yankin (CYA) ya yi alawadai da barnatawa, sacewa gami da tarwatsa wayoyin wutan da ke sada yankunan biyu da hatsabiban suka yi.

A wata takarda da babban sakataran watsa labaran shi, Mr Ebis Okpeke ya bayyana wa manema labarai, na nuna yadda shugaban kungiyar ya nuna rashin jindadinsa bisa aukuwar lamarin ba tare da zato ba, inda ya yi kira ga matasan yankin da su bar irin wannan mummunar dabi’ar, saboda hakan zai zama sanadiyyar lalacewar rayuwarsu, ta hanyar kawo cikas ga cigabansu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe