24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Osinbajo ya fi dacewa da tallar da gurguru da askirim maimakon shugabanci, Kashim Shettima

LabaraiOsinbajo ya fi dacewa da tallar da gurguru da askirim maimakon shugabanci, Kashim Shettima

Tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima wanda ke goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa ya bayyana ra’ayinsa dangane da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, LIB ta ruwaito.

A wata tattaunawa da Channels TV ta yi da shi, Shettima ya tsaya akan cewa Tinubu ya ci cancatar zama dan takarar APC na shugabancin kasa.

Yemi Osinbajo
Osinbajo ya fi dacewa da tallar da gurguru da askirim maimakon shugabanci, Kashim Shettima

Yayin da aka gwada masa sauran ‘yan takara kamar Yemi Osinbajo, Shettima ya ce duk da dai mataimakin shugaban kasar abokinsa ne kuma mutumin kirki ne, “Mutanen kirki ba sa dacewa da shugabanci.”

Ya kara da cewa, ya fi dacewa mutanen kirki su dinga siyar da gurguru da askirim ne.

Ni ne Dan takarar Shugaban Kasa da nafi kowa shiri-cewar Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shi ne dan takarar da ya fi kowa shiryawa a cikin duk masu son tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Osinbajo ya bayyana cewa shifa ashirye yake tsaf

Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Garin Yenagoa a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga majalisar sarakunan jihar a ci gaba da rangadi game da zaben shugaban kasa mai gabatowa na shekarar 2023.

Mataimakin shugaban kasar ya ce yana da kwarewar da ake bukata wajen tafiyar da harkokin kasar.

Babban makasudin ziyara ta shi ne in sanar da ku a hukumance, niyyata ta son tsayawa takarar shugabancin Tarayyar Najeriya.
“Na bayyana kudirina na son tsayawa takarar Shugaban kasa a ranar 11 ga watan Afrilu.

Dukkanmu mun sani cewa na yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa kuma cikin ikon Allah mun sami taimakon Ubangiji,zan ci gaba da kasancewa mataimakin shugaban kasa har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Burina ne ya zo a wannan rana,in ga na gaji shugaba mai ci a yanzu a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya.

A matsayina na mataimakin shugaban kasa, na yi aiki a karkashin shugaban kasa wanda ya ba ni damar ganin zahiri da idona da kuma hangen nesa kuma dama wadannan sune ake bukata wajen tafiyar da mulkin wannan kasar mai cike da sarkakiya, mai dimbin yawa.
“Na kuma taba kasancewa matsayin Shugaban kasa na rikon kwarya a lokuta da in shugaban kasa baya nan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe