28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Kwamitin tantance ‘yan takarar APC, ya kori 10 daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa

LabaraiKwamitin tantance 'yan takarar APC, ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban ƙasa

Kwamitin tantance ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kori ‘yan takara 10 daga cikin waɗanda za su fafata a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar wanda zai gudana a sati mai zuwa.

Shugaban kwamitin ya tabbatar da hakan

Shugaban kwamitin, John Oyegun, ya bayyana hakan a ranar Juma’a. A cewar rahoton Channels Tv

A cewar Mr Oyegun, 13 daga cikin ‘yan takara 26 ne kawai za su fafata a zaɓen wanda zai gudana a sati mai zuwa.

Ya ƙi ya bayyana sunayen waɗanda aka kora

Sai dai, da aka tambaye shi ko su wanene waɗanda aka hana yin takarar, Mista Oyegun ya ƙi yarda ya bayyana sunayen su.

Mista Oyegun ya kuma ƙara da cewa, saɓanin jita-jitar da ake ta yaɗawa, kwamitin bai tantance tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ba.

Kwamitin ya gudanar da tantancewar ne a tsakanin ranakun Litinin da Talata na wannan satin.

‘Yan takarar da aka tantance za su fafata a zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa a babban taron jam’iyyar wanda zai gudana a babban birnin tarayya Abuja, a tsakanin ranakun 6 zuwa 8 na watan Mayun 2022.

Zaɓen 2023: Lokacin Yarbawa ne na samar da shugaban ƙasa, Tinubu

A wani labari na daban kuma, Tinubu ya ce lokacin Yarbawa ne na samar da shugaba ƙasar nan, ya kuma ƙara da cewa kowa cikin Yarbawan shine ya dace da ya ɗare kan kujerar shugabancin ƙasar nan.

Ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa lokacin Yarbawa ne na samar da shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe. Jaridar The Punch ta rahoto

Tinubu ya bayyana hakan ne a birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget ɗin jam’iyyar APC a jihar.

Tinubu, wanda yace lokacin Yarbawa ne, ya kuma yi nuni da cewa wannan lokacin sa ne na zama shugaban ƙasa.

A cewar sa:

Wannan karon, lokacin Yarbawa ne, sannan a cikin yankin Yarbawa, lokaci na ne.

Jagoran na jam’iyyar APC na ƙasa ya samu rakiyar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, takwaran sa na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe