23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wata matar aure da ‘ya’yan ta sun biya N120,000 a halaka mahaifin su domin cin dukiyar sa

LabaraiWata matar aure da 'ya'yan ta sun biya N120,000 a halaka mahaifin su domin cin dukiyar sa

‘Yan sanda a jihar Adamawa sun cafke wata matar aure mai suna, Hafsat Saidu, da ‘ya’yan ta biyu, Faisal Saidu da Fa’iza Saidu, bisa zargin haɗa baki wajen biyan N120,000 domin a halaka mahaifin su, Saidu Mamman, mai shekaru 60 a duniya.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin


Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, wanda ya tabbatarwa da shafin LIB aukuwar lamarin, ya ce lamarin ya auku ne a gidan su dake a  Sangere FUTY cikin ƙaramar hukumar Girei ta jihar, a ranar 22 ga watan Afrilun 2022.

A cewar kakakin hukumar, matar auren wacce ta haifi yara 6 a cikin auren su da mijin ta na tsawon shekaru 30, ta tunzura yaran nata kan tsanar mahaifin na su kan cewa bai ɗauke mu su buƙatun su na yau da kullum.

Sun taɓa yunƙurin halaka shi a baya

Nguroje ya bayyana cewa waɗanda ake zargin, sun yi ƙoƙarin halaka mahaifin na su a baya amma ba suyi nasara ba bayan wani daga cikin su ya fitar da shirin su. Mahaifin na su ya kai maganar zuwa kotu inda daga baya ya janye ƙarar domin magance matsalar a cikin gida.

A ranar 22 ga watan Afrilu, Hafsat da ‘ya’yan na ta sun yi nasarar halaka shi bayan sun bayar da kwangilar kashe shi ga wani mai suna Mathew Peter (wanda aka fi sani da Goga) wanda su ka biya N120,000.

An samu mamacin kwance cikin jini da misalin ƙarfe 6 na safe, sannan akayi gaggawar kai shi zuwa asibitin ƙwararru na Yola inda aka tabbatar da mutuwar sa.

Sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi

Nguroje yace an sanar da ‘yan sanda inda su ka cafke waɗanda ake zargin da gaggawa. Ya ce dukkan su sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi, yayin da kuma wanda ya aikata kisan ya tsere a yanzu haka.

Haka kuma kakakin hukumar ya ce zaa tura waɗanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala gudanar da bincike.

Matar aure ta sheƙe mijinta har lahira kan yunkurinsa na ƙara aure

A wani labari na daban kuma, wata matar aure ta halaka mijin ta saboda yana son ƙaro aure.

A ranar Litinin 4 ga watan Afrilun 2022, wata matar aure mai ɗauke da juna biyu mai suna Omowunmi Joseph, mai shekaru 43, mai rayuwa a unguwar Odoye a yankin Alaadarin, na ƙaramar hukumar Ibadan ta arewa a jihar Oyo, ta cakawa mai gidan ta Joseph Nwanko, wuƙa har lahira da misalin ƙarfe biyu na dare yayin da yake sharar barcin sa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Tun da farko jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rigima ta barke a tsakanin ma’auratan sati biyu da su ka wuce bayan da mijin ya shaidawa matar cewa yana son yi mata kishiya daga ƙauyen sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe