26.3 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Daga zuwa yayi mata addu’a fasto yayi wa yarinya ‘yar shekara 13 fyaɗe

LabaraiDaga zuwa yayi mata addu'a fasto yayi wa yarinya 'yar shekara 13 fyaɗe

Wata babbar kotu a birnin Uyo, wacce mai shari’a, Bassey Nkanang, ke jagoranta ta tura wani fasto, Godson Thompson, mai shekaru 32 gidan kaso bisa zargin yin fyaɗe ga wata yarinya ‘yar shekara 13, wacce aka kawo wajen sa yayi mata addu’a.

An kai shi gidan kaso bayan an gabatar da shaidu

Jaridar The Punch ta rahoto cewa, alƙali Nkanang ya bada umurnin a tsare faston da ake zargin, wanda ɗan asalin garin Ikot Offiong Nsit cikin ƙaramar hukumar Nsit Ibom ta jihar Akwa Ibom, bayan ya saurari shedun da yarinyar ta kawo wacce ɗalibar makarantar sakandire ce.

Yayi mata fyaɗe bayan an kai ta wurin shi domin yayi mata addu’s

Yarinyar ta shaida wa kotu cewa yayin da take zama tare da yayar ta a birnin Uyo, mijin yayar ta ya kai ta coci inda bayan ya tafi, faston cocin ya kai ta gidan sa sannan yayi mata fyaɗe cikin tsakar dare.

Ta ce faston wanda ya haifi ‘ya’ya uku, ya bata bokiti tayi fitsari a ciki domin kada ta gudu daga gidan.

Yarinyar ta ce:

Mijin yaya ta ya kai ni wata coci a IBB Way, cikin birnin Uyo, da misalin ƙarfe  6 na yamma, inda yace zai ɗauke ni da misalin ƙarfe 7 na yamma. Bayan ya bar cocin, faston yayi kira a waya inda mai adaidaita sahu ya zo. Ya sanya na shiga ciki inda ya ke cewa zai haɗa ni da wasu mutum biyu yayi mana addu’a.

Yarinyar ta bayyana cewa, bayan sun isa gidan faston, ya ɗauko wani baƙin abu cikin ƙwalba sannan ya sha kafin yayi mata fƴaɗe.

Ta sha wahala bayan aukuwar larin

Ta cigaba da cewa, ta yi amfani da audugar mata bayan ta fara zubar da jini har na tsawon sati biyu bayan aukuwar lamarin.

Haka kuma ta ce ta ga wandunan mata kala daban-daban da hotunan mata a cikin gidan faston.

Ɗalibar wacce take a ajin SS1 ta ce ta samu ta gudu daga gidan bayan ya manta bai kulle ƙofar gidan ba. Ta samu ta gudu zuwa coci inda aka ceto ta.

Alƙali Nkanang ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa 1 ga watan Agusta na 2022 domin cigaba da gudanar da shari’a.

An tura wani mutum gidan kaso bisa yin fyaɗe ga matar aure

A wani labari na daban kuma, kotu ta tura wani mutum gidan kaso bayan yayi wa matar aure fyaɗe.

Wani mutum mai suna Mosundamola Azeez, mai shekaru 41 a duniya, an tura shi gidan maza ranar Laraba 25 ga watan Mayun 2022, bisa zargin yin fyaɗe ga wata matar aure. Shafin LIB ya rahoto.

Wanda ake zargin wanda ake tuhuma a kotu da laifin yin fyade, yayi aika-aikar ne a ranar 20 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 2 na rana.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe