24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Tsadar rayuwa ta sa mazauna Zimbabwe siyar da yatsun kafafunsu don samun na tuwo

LabaraiTsadar rayuwa ta sa mazauna Zimbabwe siyar da yatsun kafafunsu don samun na tuwo

Ana zargin Mazauna Zimbabwe da siyar da yatsun kafafunsu a dubbanin daloli saboda tsananin tsadar rayuwa tare da gaza samar da ayyukan yi a kasar, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda rahotannin kafafen sada zumunta su ka bayyana, su na siyar da manyan yatsu a $40,000 (N16,000,000), yayin da su ke sayar da kananun yatsu a $20,000 (N8,000,000). Ana kuma musayar yatsun da tsadaddun motoci.

An tattaro yadda yanzu haka maza da dama su ke ta fama wurin tafiya bayan siyar da yatsunsu a Ximex Mall da ke babban birnin kasar.

Wani lauyan Afirka ta Kudu kuma dan kasuwa, Barry Roux ya kara tabbatar da rahoton ta hanyar wallafa wani bidiyon wani mutum yayin da ya ke tafiya dakyar yayin da ya ke nuna wata tsadaddar motar da ya siya bayan sayar da dan yatsansa.

Kamar yadda ya wallafa:

“A Zimbabwe, mutane sun fara siyar da yatsunsu don siyan tsadaddun motoci. Wannan ya biyo bayan tsadar rayuwa da kuma yadda gwamnati ta gaza samar wa mutane aiki. Ana siyar da manyan yatsun a $40,000 yayin da su ke siyar da kananu da $20,000.”

Wani bidiyo wanda ya wallafa a karkashin rubutun nasa, anga wani matashi da aka bai wa makullun mota ga wani dattijo wanda aka yanke wa yatsa.

Wani mutum ma ya yi tsokaci inda ya ce yanzu haka yana jinyar yatsansa da aka cire.

Tsadar kayan abinci: ‘Yan kasuwa su taimaka su rage farashin kayan abinci kafin Ramadan, Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi, Muhammad Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya akan kawo mafita dangane da tashin farashin kayan abinci a kasar nan, LIB ta ruwaito.

Yayin jawabin rufe taron gasar karatun Al’Qur’ani mai girma da aka yi a Jihar Bauchi, ranar Asabar, 26 ga wata Maris din shekarar 2022, Sultan ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi gyara akan tabarbarewar tattalin arziki musamman ganin watan Ramadan ya karato.

Basaraken ya tunatar da shugabannin siyasa cewa ‘yan Najeriya sun zabe shi ne don su yi musu aiki, ya roki masu sayar da kayan abinci akan su sassauta farashin kayan abinci lokacin azumi.

Kamar yadda yace:

“Ina tunanin ya rage mana akan mu hade kawunanmu don yin aiki akan tashin farashin kayan abinci, saboda kowa ya samu ya siya a lokacin Ramadan.

“Na yarda da cewa wannan bukatar bata gagari gwamnati ba. Don mun zabe su ne don suyi mana aiki ba wai muyi musu aiki ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe