28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Tsagerun Kamaru su afko Najeriya, kawo yanzu sun halaka mutane 20

RikiciTsagerun Kamaru su afko Najeriya, kawo yanzu sun halaka mutane 20

‘Yan ta’addan Ambazonia, wata kungiyar tsageru ta Kudu maso Yammacin Kamaru, sun halaka akalla mutane 20 a wani gari da ke karamar hukumar Boki a Jihar Cross River.

Tsohon dan majalisar tarayya kuma dan takarar dan majalisar wakilai na mazabar Boki/Ikom, Chief Cletus Obun ne ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ya auku ne a ranar Lahadi.

Kamar yadda ya bayyana:

“Zan iya tabbatar da cewa sojojin Ambazonia ne su ka auko iyakar Najeriya da safiyar Lahadi don kai wa ‘yan uwansu da su ka shigo Najeriya ko su ka ki shiga kungiyarsu farmaki.

“Sun halaka kusan mutane 20. Babu wanda ya tabbatar ko akwai ‘yan Najeriya a cikin wadanda su ka halaka.”

Ya ce sauran ‘yan Kamarun da su ke yaren Bokye na mutanen Boki su shigo garin Bashu, bai yi nisa da Danare ba, inda rundunar sojin Najeriya ta kafa karamin sansani.

Mayakar Ambazonia su ka shigo Boki, wurin da mutanen Kamaru da dama su ke zama don tayar da tarzoma.

Yayin da aka nemi jin ta bakin jami’an rundunar soji na 13 Brigade da ke Calabar, Kaftin Tope Aluko bai tabbatar da harin kwannan ba, amma ya ce makamancin hakan ya faru watanni 6 da su ka gabata bayan sun afka Jihar Taraba.

Mataimin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya bayyana batun harin da mayakan Kamarun su ka kai wani kauye da kuma wasu yankuna a Manga cikin Jihar Taraba.

Dan majalisar ya ce tsagerun Kamaru ne su ka tayar da hankula a kauyen.

Bwacha ya na wakiltar Taraba ta kudu ne a majalisar wakilai, kuma ya ce har yanzu dai ba a san manufarsu ba.

Kamar yadda ya ce:

“Na farka da safiyar nan inda na samu bayani daga mutanen kasar mu da jami’an tsaro akan mummunan lamarin da ya taba martabar kasarmu. Karamar hukumar Takum, wacce Bataliyar sojin Najeriya ta 23 ke zama, su na fuskantar hari. Don haka mai girma shugaban kasa ya kamata sojojin Najeriya su tashi don kawo karshen wannan farmakin kuma su dakatar da tsagerun daga fadada dabarsu.

“Har yanzu dai ba a san manufar tsagerunsu ba, ko dai su na da niyyar fadada dabarsu mo kuma su na neman kwace yankin ga Kudu maso Yammacin Kamaru.”

‘Yan bindiga sun halaka magidanci, sun ɗauke iyalan tsohon kwamishina a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun kai hari a garin Jere cikin ƙaramar hukumar Kagarko, a jihar Kaduna, inda su ka halaka wani magidanci da yayi ƙoƙarin hana su tafiya da matar sa mai ɗauke da juna biyu. Jaridar Vanguard ta rahoto.

‘Yan bindigan na ɗauke da muggan makamai

Sun zo da yawa, sama da mutum 50, ɗauke da muggan makamai. Mutumin yayi ƙoƙarin hana ‘yan bindigan tafiya da matar sa inda su ka halaka shi. Matar na ɗauke da juna biyu. A cewar wani mazaunin ƙauyen.

An shaida wa ‘yan jarida cewa yan bindigan kuma sun kai hari gidan wani tsohon kwamishina inda su ka tafi da mutum huɗu.

Akan babura su ka zo, sun fi mutum 50. Mun ɓoye sanda mu ka ga suna tafiya zuwa gidan. Kamar dama sun san gidan tsohon kwamishinan, sun je gidan inda su ka ɗauke yan’uwan sa mutum 4. Cikin sa’a baya cikin garin Jere, amma sun tafi da matar sa, wata ƙaramar yarinya, ƙanwar sa da kuma ƙanwar matar sa.

Ɗayan mutumin yana kokowar ƙwato matar sa daga hannun ‘yan bindigan. Sun halaka shi inda su ka buɗe masa wuta. Mun ji cewa ‘yan sanda sun bi su inda su ka halaka mutum biyu daga cikin ‘yan bindigan.

Matasa na shirin gudanar da zanga-zangar lumana

Akwai tashin hankali a Jere saboda matasa sun nuna ɓacin ran su kan yawaitar hare-haren da ake kawowa garin. Suna son gudanar da zanga-zangar lumana.

Hukumar ‘yan sanda bata ce komai ba dangane da rahoton lamarin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe