22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ko me yayi zafi: ‘Yan acaɓa sun cinnawa gidaje wuta a Abuja

LabaraiKo me yayi zafi: 'Yan acaɓa sun cinnawa gidaje wuta a Abuja

Sama da ‘yan acaɓa mutum 100 ne su ka dira a rukunin gidajen Same Global Estate a yankin Lokogoma cikin birnin tarayya Abuja domin ɗaukar fansar abokan aikin su mutum biyu da aka halaka.

‘Yan acaɓar sun je ɗaukar fansa ne

Lamarin ya auki ne bayan wani mai babur ya buge ‘yan acaɓar a ranar Lahadi sannan ya gudu zuwa cikin rukunin gidajen domin neman mafaka.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa ‘yan acaɓar sun cinnawa gidaje biyu wuta a yankin.

Mazauna rukunin gidajen sun bayyana cewa ‘yan acaɓar sun kai hari wurin ne domin kama wani mai babur wanda ba’a san kowane ne ba.


Sun lura da cewa an mutane da dama sun biyo mai babur ɗin bayan ya buge ‘yan acaba biyu.

Jami’an tsaro sun garzaya zuwa wurin domin hana cigaba da lalata kadarori.

An bayyana yadda lamarin ya auku

Manajan rukunin gidajen Mr Adebisi Adelowo, wanda yayi magana da jaridar Punch, ya bayyana cewa:

Sama da ‘yan acaɓa 100 su ka dira a rukunin gidajen mu sa’o’i kaɗan da su ka wuce. Sun yi ƙoƙarin ƙona wurin ta hanyar cinnawa gidaje biyu wuta.

Sun ɓalle mana ƙofa inda su ka fara jifa cikin gidajen mutane. Mun ƙasa tsayar da su har sai da ‘yan sanda da sojoji su ka kawo ɗauki.

Daga baya mun fahimci cewa sun dira a wurin mu ne saboda wani mai babur ya shigo neman mafaka a wajen bayan ya buge abokan aikin su mutum biyu inda su ka rasa ran su. Sun biyo shi da duwatsu da kuma muggan makamai.

Mai babur ɗin wanda ba mazaunin wurin bane ya shigo ne bayan ya lura da akwai allon ‘yan sanda a gaban rukunin gidajen

Wasu ɓata gari sun cinnawa wani matashi wuta saboda canjin N100

A wani labari na daban kuma, wasu ɓata gari sun cinnawa wani matashi wuta saboda canjin 100 a birnin Legas.

Ana zargin wasu ‘yan acaɓa da cinnawa wani matashi wuta a jihar Legas. Shafin LIB ya rahoto

Matashin mutumin mai suna David, an yi masa dukan tsiya sannan aka cinna masa wuta wacce tayi sanadiyyar ajalin sa.

Ana zargin cewa David ya samu saɓani ne da wani ɗan acaɓa kan canjin naira 100. Hakan ya sanya faɗa barkewa tsakanin David da ɗan acaɓan. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe