27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

‘Yan bindiga sun halaka magidanci, sun ɗauke iyalan tsohon kwamishina a jihar Kaduna

Labarai'Yan bindiga sun halaka magidanci, sun ɗauke iyalan tsohon kwamishina a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun kai hari a garin Jere cikin ƙaramar hukumar Kagarko, a jihar Kaduna, inda su ka halaka wani magidanci da yayi ƙoƙarin hana su tafiya da matar sa mai ɗauke da juna biyu. Jaridar Vanguard ta rahoto.

‘Yan bindigan na ɗauke da muggan makamai

Sun zo da yawa, sama da mutum 50, ɗauke da muggan makamai. Mutumin yayi ƙoƙarin hana ‘yan bindigan tafiya da matar sa inda su ka halaka shi. Matar na ɗauke da juna biyu. A cewar wani mazaunin ƙauyen.

An shaida wa ‘yan jarida cewa yan bindigan kuma sun kai hari gidan wani tsohon kwamishina inda su ka tafi da mutum huɗu.

Akan babura su ka zo, sun fi mutum 50. Mun ɓoye sanda mu ka ga suna tafiya zuwa gidan. Kamar dama sun san gidan tsohon kwamishinan, sun je gidan inda su ka ɗauke yan’uwan sa mutum 4. Cikin sa’a baya cikin garin Jere, amma sun tafi da matar sa, wata ƙaramar yarinya, ƙanwar sa da kuma ƙanwar matar sa.

Ɗayan mutumin yana kokowar ƙwato matar sa daga hannun ‘yan bindigan. Sun halaka shi inda su ka buɗe masa wuta. Mun ji cewa ‘yan sanda sun bi su inda su ka halaka mutum biyu daga cikin ‘yan bindigan.

Matasa na shirin gudanar da zanga-zangar lumana

Akwai tashin hankali a Jere saboda matasa sun nuna ɓacin ran su kan yawaitar hare-haren da ake kawowa garin. Suna son gudanar da zanga-zangar lumana.

Hukumar ‘yan sanda bata ce komai ba dangane da rahoton lamarin.

Kaduna : ‘Yan bindiga sun halaka mutane 360, sun yi garkuwa da 1,389 a cikin watanni 3 – Rahoto

A wani labari na daban kuma, wani rahoto ya bayyana adadin yawan mutane da ‘yan bindiga su ka halaka da kuma waɗanda su kayi garkuwa da su a jihar Kaduna.

Rahoton ya ce sojojin kasa sun kashe ‘yan bindiga 41 yayin da aka kashe sama da 60 ta hanyar wasu hare-hare ta sama da aka kai a wasu sansanonin ‘yan bindiga da ke cikin jihar, Premium Times ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 360 ​​a rubu’in farko na shekarar 2022 (Janairu – Maris) a jihar Kaduna, wani rahoton tsaro da gwamnatin jihar ta fitar

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe