28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Samari dama ta samu: Baturiya na cigiyar miji, ta ce dan Afirka take so

LabaraiLabaran DuniyaSamari dama ta samu: Baturiya na cigiyar miji, ta ce dan Afirka take so

Fah Onpatchara, wata mata ce ‘yar kasar Thailand wacce tayi fice a kan irin kaunar da take wa Afirka da mutanen cikin ta. Matar mai shekaru 30 wacce tayi fice a Abenna a kafafan sada zumuntar zamani, a cewarta abokan ta na kasar Ghana ne suka sa ma ta, wanda ke nufin mace da aka haifa ranar Talata, ta bayyana yadda take matukar kaunar Kenya, LabarunHausa.com ta ruwaito.

Matar ‘yar kasar Thailand wacce aka fi sani da Abenna ta bayyana matukar kaunar da take wa mazan Afirka tuntuni amma yanzu bata soyayya.

Yayin jawabi a wata tattaunawa da manema labaran Tuko.co.ke, ta yabi Kenya a matsayin kasa mai matukar kyau, sannan mutanen ciki na da karamci da kara.

“Ina da kawaye da dama a kasashen Afirka da dama. Amma ‘yan kasar Kenya sun fi nuna min so da kauna.
A duk lokacin da na hadu dasu, ji nake kamar ‘yan uwana ne,” a cewarta.

Matar ‘yar kasar Thailand na da zanen tambarin Kenya a gefen kwankwasonta na hagu da kuma zanen taswirar Afirka a kwankwasonta na dama.

“Na zana tambarin Kenya da taswirar Afirka ne bayan an gayyace ni wani taron a ranar bikin Jamhuri na ‘yan kasar Kenya a Thiailand a ranar 11 ga watan Disamba, 2021, hakan yasa nayi alfahari da kaina, tare da ga ganin irin kaunar da nake wa ‘yan Kenya da ‘yan Afirka wadanda suka halarci taron,” a cewarta.

Nayi zanen ne don tunatar da kaina yadda ‘yan kasar Kenya da ‘yan Afirka ke kaunata,” ta bayyana hakan.

Matar dake zaune a Thailand ta ce Kenya kamar dayan gida ne a gun ta, kuma zata so ta kara ziyartar masoyanta.

“Na koyi manyan kalmomin Kiswahili kuma ina saran kayan wasu da dama,” a cewarta.

Ta kara da cewa: “Bazan gaji da Kaunar dukkan ‘yan Kenya ba. Ina farincikin kasancewa cikin ku. Nawapenda sana.”

Da aka tambayeta ko tasan wani fitacce ko mawaki a kasar Kenya? da wakar da tafi so, kyakyawar matar kai tsaye ta ce;

“Wakar Malaika da Nyashinski ya yi ita ce farkon wakar da na fara sani. Kuma har yanzu ita ce wakar da nafi so.”

Abenne ta ce har yanzu bata da tsayayye

Taurawurar budurwar, wacce ake yawan sanya hotunanta a tutar Kenya, ta bayyana yadda a baya tayi soyayya da wani mutumi ‘dan kasar Afirka, amma yanzu bata da tsayayye.

“A halin yanzu bana neman mashinshini. Kawai ina bukatar abokai da kawaye a yanzu, amma naso a ce na auri ‘dan Afirka, amma hakan sa a nema. Bazan iya zabar kasa ba,” a cewarta.

Baturiyar da ta halaka saurayinta dan Najeriya a kasarsu ta ci gaba da walwalarta, har da zuwa mashaya

An ga wata baturiya da ta halaka saurayinta dan Najeriya ta hanyar daba masa makami a mashaya tana shan giya tare da mahaifinta, yayin da dangin wanda ta halakan suke zaman makoki, LIB ta ruwaito.

Courtney Tailor Clenney ta halaka Christian Toby Obumseli, dan Najeriya sannan mazaunin Amurka ta hanyar daba masa wuka a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu, a mazauninsu dake Miami.

Anyi ram da Courtney, amma sai tayi barazanar halaka kanta, hakan yasa ‘yan sanda suka mikata ga asibitin mahaukata karkashin dokar Baker.

A Florida, jami’an tsaro na da damar mika mutum asibitin mahaukata na tsawon kwanaki uku ta hanyar amfani da dokar kasa ta Baker.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe