23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Wani mutum ya kashe N5.6m don ya koma kare

LabaraiLabaran DuniyaWani mutum ya kashe N5.6m don ya koma kare

Mutane sun dinga kiran wani mutum da mai wauta akan yadda ya kashe £12,500 wanda ya yi daidai da Naira Miliyan 5.6 don ya koma kare, LIB ta ruwaito.

Mutumin dan asalin kasar Japan ne kuma ya je har Tokyo don ya mayar da kansa kare da taimakon masu hada kayan.

KARE
Wani mutum ya kashe N5.6m don ya koma kare

An kai masa kayan kare a watan da ya gabata inda ya dinga yada bidiyonsa sanye da kayan karen ya na rawar wakar karnuka.

Bidiyon nasa sun nuna yadda ya dinga juyi a kasa kuma ya na amsa umarni tamkar kare.

A bidiyonsa na farko ya bayyana cewa:

“Na zama collie ne saboda ina son komawa dabba. Amma yanz ina ta tunanin yada bidiyona”, a cewarsa.

Kamar yadda labarun Japanese su ka nuna, ya kashe £12,500 inda ya siya kayan karnukan daga Zeppet wanda ya ke shirya kayan dabbobi don fina-finai.

Bidiyoyin nasa sun janyo surutai daga mutane da dama.

Yayin da wasu su ka dinga yaba masa, wasu kuma sun ga wautarsa.

“Kalli wata sakarar hanyar kashe kudi! Amma ya yi kamar karen gaske, kamar kyakkyawan kare. Ina gaisuwa,” kamar yadda wani ya yi tsokaci.

“Wannan ai wauta ce,” inji wani.

Bidiyon wani kare da yake kaɗa fiyano yana rera waka ya ɗauki hankali a yanar gizo

Bidiyon wani kare yana kara matukar daukan hankali a soshiyal midiya, wanda a cikin sa aka ga wani kare yana kada fiyano.

Shafin Updatefever ya tattaro cewa abin da ya fi komai ban mamaki shine, karen yana kada fiyano kuma yana rera waƙa.

Mutane da dama sun kalli bidiyon karen

An yada bidiyon wannan kare ne a wani tashar Youtube mai suna Buddy Mercury, inda mutane sama da miliyan biyu suka kalla, mutum 27, 000 kuma su ka danna alamar so, a kan bidiyon.

A wannan bidiyon na karen, za’a iya ganin sa ya dora hannayen sa akan madannan sautin fiyanon, inda yake amfani da taintaiyar hannun sa wajen danna su, sai kuma karen ya rera wakar sa idan sautin da ya danna yayi ƙara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe