27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Muhammad Abacha ya lashe zaben fidda gwani na takarar gwamna a jamiyyar PDP a Kano

LabaraiMuhammad Abacha ya lashe zaben fidda gwani na takarar gwamna a jamiyyar PDP a Kano

Alhaji Muhammad Abacha, ɗan tsohon shugaban kasa na soja, janar Sani Abacha, ya lashe zaben fidda gwani na takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023 a jihar Kano. Jaridar The Nation ta rahoto

Muhammad Abacha ya lashe zaɓen da tazara mara yawa sosai

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, (NAN) ta tattara rahoton cewa, Abacha ya sami kuri’a 736 inda ya kayar da abokin takarar sa Jafar Sani-Bello, wanda ya sami kuri’a 710 a zaɓen fidda gwanin, wanda aka yi a ranar Laraba a jihar Kano.

Da take sanar da sakamakon zaben, jami’ar zaben Hajiya Amina, ta ayyana Abacha a matsayin wanda ya lashe zaben, da kuri’u 736.

Hukuma ta tabbatar da halascin zaɓen

Shugaban hukumar zaɓe, Alhaji Mohammed Jamu, yace an gudanar da zaɓen da halastattun tawagar wakilai, wanda ya sami sanya ido daga jami’an hukumar zabe ta INEC, yan sanda, da kuma sauran hukumomin tsaro, a fadar (NAN) din.

Jigawa 2023: Ɗan Sule Lamido ya lashe zaɓen fidda gwanin PDP na ‘yan takarar gwamna

A wani labari na daban kuma, ɗan Sule Lamido, Mustapha Sule Lamido ya lashe zaɓen fidda gwani na PDP na ‘yan takarar gwamna a jihar Jigawa. Mustapha ya lallasa abokin karawar sa da tazara mai nisa.

An zabi ɗan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a matsayin ɗan takarar kujerar gwamna a ƙarƙashin inuwar jambiyyar adawa ta PDP, a ranar Laraba a jihar. Jaridar Premium Times ta rahoto

Mustapha Sule Lamido ya ba abokin hamayyar sa tazara mai nisa

Mustapha Lamido ya kayar da abokin karawar sa, Sale Shehu, tsohon ƙaramin ministan ayyuka da ƙuri’u 829 da babu ko ɗaya. An samu ƙuri’u uku marasa kyau.

Shugaban kwamitin zaɓen, Isah Ahmad, ya taya wanda yayi nasara murna tare da sauran wakilan jam’iyya bisa gudanar da zaɓen cikin nasara. Yace zaɓen ya gudana cikin lumana da inganci.

Haka kuma a yayin jawabin sa, Mustapha Sule Lamido yace:

Dole na ƙarɓi wannan zaɓen da ku kayi min da tawali’u, juriya da kuma jajircewa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe