24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

An tura wani mutum gidan kaso bisa yin fyaɗe ga matar aure

LabaraiAn tura wani mutum gidan kaso bisa yin fyaɗe ga matar aure

Wani mutum mai suna Mosundamola Azeez, mai shekaru 41 a duniya, an tura shi gidan maza ranar Laraba 25 ga watan Mayun 2022, bisa zargin yin fyaɗe ga wata matar aure. Shafin LIB ya rahoto.

Wanda ake zargin wanda ake tuhuma a kotu da laifin yin fyade, yayi aika-aikar ne a ranar 20 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 2 na rana.

An bayyana lokacin da lamarin ya auku

Azeez wanda yayi fyaɗe ga matar auren mai shekaru 30 a duniya, ya aikata laifin ne a sansanin Budo Iseyin kusa da wani gari mai suna Saki. Laifin sa ya dai karya sashi na 357 sannan kuma abin hukuntawa ne a sashi na 358 na dokar masu aikata laifi ta jihar Oyo ta shekarar 2000.

Alƙaliyar kotun majistare, Munirat Giwa-Babalola, tayi watsi da roƙon wanda aƙe ƙarar inda ta bayar da umurnin a tsare shi a wani gidan kaso dake a Agodi.

Sannan kuma kotun ta ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa 1 ga watan Agusta.

Ana samun yawaitar fƴaɗe a Najeriya

Ana samun yawaitar fyade a Najeriya duk kuwa da ƙasar na da dokokin da su kayi hani da aikata fƴaɗe.

Masana na ganin cewa akwai buƙatar s ƙara tsaurin hukuncin masu aikata fyaɗe a Najeriya. A ganin su yin hakan ka iya kawo raguwar aikata laifin a ƙasar.

Mutanen da aka yiwa fƴaɗe dai suna shiga cikin halin ƙuncin rayuwa, baƙin ciki da takaici saboda fƴaɗen da aka yi mu su.

Ke duniya: Malamin makaranta yayi wa ɗalibar sa mai shekaru 13 fyade

A wani labari na daban kuma, wani malamin makaranta ya yi fƴaɗe ga ɗalibar sa. Malamin dai ya aikata laifin ne akan ɗalibar ajin sa mai shekaru 13 kacal a duniya.

Wani malamin makaranta mai shekaru 25, a wata makarantar firamare a Ago Iwoye, jihar Ogun, ya shiga hannun hukuma a ranar 19 ga watan Mayu, bisa zargin yin amfani da wata yarinya mai shekaru 13 (an ɓoye sunan ta) wacce ɗaliba ce a ajin sa.

Shafin LIB ya rahoto cewa malamin wanda ake zargi, Ayobami Oluwatobiloba Runsewe, an cafke shi bayan shigar da koke a ofishin ‘yan sanda na Ago Iwoye daga wurin mahaifiyar wacce taje da yarinyar, inda ta bada rahoton cewa malamin ya yaudari yarinyar zuwa gidan sa dake a unguwar Ayehbami cikin Ago Iwoye bayan an tashi daga makaranta da misalin ƙarfe 4:30 na yamma inda yayi amfani da ita ta ƙarfin tsiya

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe