28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Buhari ya gana da waɗanda bam ya tashi da su a Kano, ya nuna matuƙar jimamin sa

LabaraiBuhari ya gana da waɗanda bam ya tashi da su a Kano, ya nuna matuƙar jimamin sa

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi da su a jihar Kano, domin yi mu su gaisuwa da yawun yan kasa baki daya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa shuugaban ƙasar ya bayyana lamarin, wanda mutane a kalla tara 9 suka mutu, 22 kuma su ka jikkata suke karbar kulawa a asibiti, da cewa abin baƙin ciki ne kuma abin takaici.

An tabbatar da ganawar shugaba Buhari da iyalan waɗamda abon ya ritsa da su

Babban mai taimawa shugaban kasar ta fannin kafar yada labarai, Malam Garba Shehu, shine ya tabbatar da ganawar shugaban kasar da iyalan waɗanda abin ya shafa a ranar Litinin a Abuja.

Iyalan wadanda abin ya shafa a unguwar sabon gari wadanda su ka haɗa da Chief Nicholas Ibekwe, da Eze Igbo, an tara su ne a fadar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero domin haɗuwa da shugaban kasar.

Shugaban wanda yazo Kano domin murnar cika shekara 58 na hukumar sojojin Najeriya, wanda bayan ya kammala ya fara da kai ziyarar gaisuwa zuwa fadar.

Yayi matuƙar kaɗuwa dangane da lamarin

A wani gajeren jawabi, shugaban kasar yace:

Yayi matukar bakin ciki sakamakon rasa rayuka da raunuka ga mutane da yawa, a sanadiyyar tashin bam din.

Tunani na da na ‘yan kasa yana tare da iyalan da wannan abu ya shafa. Ina fata wadanda suka samu raunuka za su sami sauki cikin kankanen lokaci

A karshe, shugaba Buharin ya bayyana fadar Kano a matsayin gida a gareshi.

Sinadarin haɗa bam ne, ‘yan sanda sun yi amai sun lashe, sun bayyana haƙiƙanin abinda ya fashe a Kano

A wani labari na daban kuma ‘yan sanda sun yi amai sun lashe kan haƙiƙanin abinda ya fashe a Kano. Da farko dai ‘yan samda sun bayyana cewa tulun gas ne ya fashe

Rundunar yan sanda ta jihar Kano, tace karar fashewar da aka ji a ranar 17 ga watan Mayu, wacce ta haddasa mutuwar mutane 9 a yankin unguwar sabon gari dake jihar Kano, ta faru ne sakamakon amfani da wasu sinadarai domin haɗa bam haɗin gida. Jaridar Daily Nigerian ta rahoto

Tun farko, yan sandan sun bayyana cewa, tulun gas ne ya haddasa fashewar, amma daga baya sai su ka ce, fashewar ta faru ne a shagon da ake haramtaccen kasuwancin sayar da sinadaran da ake hada bam dasu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe