27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Cikin shekara daya, ma’aikatan jinya 7,256 ‘yan Najeriya sun tsere Birtaniya

LabaraiCikin shekara daya, ma’aikatan jinya 7,256 ‘yan Najeriya sun tsere Birtaniya

Aƙalla ma’aikatan jinya 7,256 da aka horar da su a Najeriya sun koma Burtaniya tsakanin Maris 2021 da Maris 2022, in ji jaridar PUNCH.

Alƙaluman na ƙunshe ne a cikin bayanan da aka samu daga hukumar kula da aikin jinya da ungozoma ta ƙasar Burtaniya ranar Alhamis.

Jaridar PUNCH ta rahoto cewa Najeriya na ci gaba da samun ƙaruwar ma’aikatan lafiya da ke ƙaura daga ƙasar.

Alƙaluman sun nuna cewa ma’aikatan jinya 2,796 ‘yan Najeriya ne suka yi hijira zuwa ƙasar Burtaniya tsakanin watan Maris na 2017 zuwa Maris 2018 yayin da aka samu kwararar ma’aikatan jinya 3,021 zuwa ƙasar Burtaniya tsakanin watan Maris na 2018 da Maris 2019.

Majalisar ta yi nuni da cewa an samu ƙaruwa a tsakanin Maris 2019 da Maris 2020 lokacin da jimillar ma’aikatan jinya 3,684 ‘yan Najeriya suka yi hijira zuwa Burtaniya.

A cikin 2020, yayin da cutar ta COVID-19 ta yi ƙamari, ma’aikatan jinya 4,310 na Najeriya sun yi rajista da majalisar tsakanin Maris 2020 da Maris 2021.

Duk da haka, majalisar ta shaida mafi girman adadin rajista a cikin shekaru biyar da suka gabata lokacin da jimillar ma’aikatan jinya 7,256 da aka horar da su a Najeriya suka yi rajista tsakanin Maris 2021 da Maris 2022.

Majalisar ta ce, “Mutanen da suka sami horo a Philippines da Indiya suna ci gaba da wakiltar wani kaso mai tsoka na rajistar mu na dindindin kuma suna ba da gudummawa sosai ga ci gabanmu na shekara.

“Tsakanin 2021 zuwa 2022, an sami ƙaruwar yawan mutanen da suka samu horo a Indiya, Philippines da Najeriya da suka shiga rajista na dindindin a karon farko.”

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku a yawan masu horar da ma’aikatan jinya daga ƙasashen waje a Burtaniya, bayan Philippines da Indiya.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta ƙasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta daidaita tafiye-tafiyen ma’aikatan jinya da ungozoma a ƙasar, inda ta yi nuni da cewa hakan na yin illa ga fannin kiwon lafiya a Najeriya.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ci gaba da bayar da shawarar kyautata yanayin aiki ga likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya a wani yunƙuri na daidaita fitar da jarin dan Adam zuwa ƙasashen waje.

Abin al’ajabi: Ma’aikatan lafiya 11 a wani asibiti sun samu juna biyu a tare, 2 daga ciki rana ɗaya za su haihu

Ma’aikatan lafiya mutum 11 masu aiki a wani asibitin birnin Missouri, suna ɗauke da juna biyu a lokaci ɗaya, inda biyu daga cikin ma’aikatan jinya daga cikin su, ake sa ran haihuwar su a rana ɗaya. Shafin LIB ya rshoto

A asibitin Liberty Hospital cikin Liberty, birnin Missouri, ma’aikatan jinya 10 da wata likita guda ɗaya suna ɗauke da juna biyu inda ake sa ran haihuwar su cikin watanni masu zuwa.

Da dama daga cikin su aiki ne a ɓangare guda

Da yawa daga cikin ma’aikatan lafiyan masu ɗauke da juna biyun, suna aiki ne a sashin unguwar zoma da kuma karɓar haihuwa.

Darektan ɓangaren karɓar haihuwa, Nicki Kolling ya shaida wa Fox4 KC cewa:

Koda yaushe suna yin abubuwan su rukuni-rukuni, amma ba mu taɓa samun guda 10 a lokaci ɗaya ba, saboda haka wannan abin raha ne.

Ko a baya an taɓa samun irin haka

Wannan dai ba shine karon farko ba da wani asibiti ya samu ma’aikatan sa da dama na ɗauke da juna biyu a lokaci daya ba.

A shekarar 2019, ma’aikatan jinya 9 masu aiki a ɓangaren karɓar haihuwa a asibitin Maine Medical Center, suna ɗauke da juna biyu a lokaci ɗaya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe