23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ke duniya: Malamin makaranta yayi wa ɗalibar sa mai shekaru 13 fyade

LabaraiKe duniya: Malamin makaranta yayi wa ɗalibar sa mai shekaru 13 fyade

Wani malamin makaranta mai shekaru 25, a wata makarantar firamare a Ago Iwoye, jihar Ogun, ya shiga hannun hukuma a ranar 19 ga watan Mayu, bisa zargin yin fyaɗe ga waya yarinya mai shekaru 13 (an ɓoye sunan ta) wacce ɗaliba ce a ajin sa.

Malamin ya yaudari yarinyar zuwa gidan sa

Shafin LIB ya rahoto cewa malamin wanda ake zargi, Ayobami Oluwatobiloba Runsewe, an cafke shi bayan shigar da koke a ofishin ‘yan sanda na Ago Iwoye daga wurin mahaifiyar wacce taje da yarinyar, inda ta bada rahoton cewa malamin ya yaudari yarinyar zuwa gidan sa dake a unguwar Ayehbami cikin Ago Iwoye bayan an tashi daga makaranta da misalin ƙarfe 4:30 na yamma inda yayi mata fyade ta ƙarfin tsiya.

An taho da wandon yarinyar mai cike da jini a matsayin sheda a ofishin na ‘yan sanda

Bayan karbar koken, DPO ɗin Ago Iwoye, , SP Noah Adekanye, ya tura jami’an sa zuwa gidan inda aka cafke malamin.

Yayin da ake tuhumar sa, da farko ya ƙaryata yi wa yarinyar fyaɗe amma da aka gabatar da yarinyar sai ya rasa bakin magana.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, yace an tura wanda ake zargin zuwa sashin hana safarar mutane da sa ƙananan yara aiki na hukumar domin cigaba da gudanar da bincike.

Ke duniya: Uba ya ɗirkawa ‘yar cikin sa mai shekaru 15 ciki bayan yayi mata fyaɗe

A wani labari na daban kuma, wani uba yayi wa ‘yar sa ciki bayan yayi mata fyaɗe. Mahaifin yayi yunkurin zubar da cikin kafin a cafke shi.

An cafke wani mutum mai shekaru 38 a duniya bisa laifin aikata fyaɗe ga ‘yar cikin sa mai shekaru 15 a duniya a jihar Ondo. Shafin LIB ya rahoto.

An cafke wanda ake zargin

‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargin, Sunday Udoh, bayan yayi yunƙurin zubar da cikin da yarinyar ta samu bayan ya sadu da ita.

Udoh ya kai ɗiyar ta sa zuwa wani asibiti a Ile-Oluji, domin a zubar da cikin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe