23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Zan gyara Najeriya cikin wata 6 kacal, ɗan takarar shugaban ƙasa

LabaraiZan gyara Najeriya cikin wata 6 kacal, ɗan takarar shugaban ƙasa

Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, Anyim Pius Anyim, ya bayyana cewa cikin wata shida zai gyara Najeriya, idan aka zaɓe shi shugabam ƙasa a zaɓen 2023.

Ɗan takarar yayi jawabin ne a Jigawa

Anyim ya bayyana hakan ne yayin da yakai ziyara ga ƙusa a jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a jihar.

A bayanin da jaridar Punch ta samu ranar Lahadi, tsohon shugaban majalisar yayi alƙwarin daidaita lamuran ƙasar nan cikin wata 6 sannan da kuma shirya cigaban ta.

Nayi alƙwarin cewa cikin wata 6 na farkon gwamnati na, zan daidaita lamuran ƙasar nan sannan zan shirya ta domin samun cigaba, zaman lafiya da wadata.

Ya bayyana wa Lamido

Anyim ya ƙara da cewa:

Dole ne mu yarda akan abubuwan da su ka raba mu. Dole ne mu san abubuwan dake aiki a tsakanin mu. Zan samar da hanyar cimma hakan.

Za mu yi aiki tare domin dawo da martabar Najeriya. Zan samar da wannan shugabancin wanda zai samar da maslaha a ƙasa sannan ya daidaita tsakanin ‘yan Najeriya.

Yayi wani muhimmin alƙawari ga jihar

Tunda farko yayin da yake magana a sakatariyar jam’iyyar domin jawo hankalin deliget, Anyim yayi alƙawarin mayar da jihar Jigawa cibiyar fitar da amfanin gona ƙasashen waje, inda yayi nuni da cewa Najeriya na da abubuwan koyo sosai daga jihar.

Jihar Jigawa bayan kayan amfanin gona, na da abubuwan kai wa sauran sassan Najeriya. Jigawa ita kaɗai ce jiha a Najeriya wacce ba matsalar tsaro sannan kuma ba barazanar matsalar tsaro

A cewar Anyim

2023: Maza sun gaza; cikin watanni 6 zan dawo da Najeriya kan turba, ‘yar takarar shugaban ƙasa

A wani labari na daban kuma, ‘yar takarar shugaban ƙasa ta ce maza sun gaza, za ta dawo da ƙasar akan turba cikin wata 6 kacal.

Yar takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Uju Ken Ohanenye, ta nuna damuwar ta kan abinda ta kira da gazawar maza wajen samar da shugabanci mai kyau a Najeriya. Jaridar Vanguard ta rahoto

A yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tv a Legas, ranar Laraba, ‘yar takarar tayi nuni da cewa za ta kawo ƙwarewa da ɗaɓi’ar uwa wajen mulki domin kawo sauyi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe