29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Yadda direban Napep zai yi wuff da zukekiyar budurwa bayan shekaru 5 da amsar lambarta

LabaraiYadda direban Napep zai yi wuff da zukekiyar budurwa bayan shekaru 5 da amsar lambarta

Wata budurwa ‘yan Najeriya mai suna Lydiv Ogbansiegbe ta bayyana irin natsuwar da mutum ke samu idan ya hadu da abokin rayuwar da ya dace dashi. Lydiv ta wallafa wannan ra’ayin nata ne yayin da ta bayyana sa ranar aurenta da masoyinta a shafin Instagram da hoton bikin sa ranar, Legit.ng ta ruwaito.

Yadda Lydiv ta hadu da shi tare da tuna yadda suka fara soyayya, kyakyawar budurwar ta bayyana yadda suka fara haduwa a kan adaidaita sahu.

Lydiv ta ce, ta ba wa mai adaidaita sahu lambar wayarta shekaru biyar da suka wuce, sannan a halin yanzu wannan mutumin ne ya roketa ta aureshi.

Ta rubuta:

“Akwai irin yanayin nan na natsuwa dake zuwa maka idan mutumin ya dace dakai.
“Shekaru biyar da suka shude na bada lambar wayata ga mai adaidaita sahu.

“Labarin soyayyar nada tsawo. Kaunar da nake maka bata da adadi nawa.”

‘Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu:


@comedian_aboki44 ya ce:

“Ina tayasu murna, soyayya abune mai dadi idan ka hadu da wanda ya dace dakai.”

theunlimitedmusic ya ce:

“Babu fashin baki a wannan labarin amma ina muku murna. Kawai abun da ya dace shine mutum ya siya adaidaita fa. Kila nima zan hadu da mai sona da gaske. Koda yake na manta haduwa yafi haka.”


@official_soicm ya ce:

“Kawai ya kamata mutum ya fara tuka adaidaita. Waye keda keke da zan dinga kawo mai kudi duk karshen sati.”

Yadda wani ango ya fatattaki amaryar sa bayan ya gano cewar ba budurwa ba ce watanni 4 bayan auren su

Wani dan Najeriya ya yanke igiyar auren sa da amaryar sa bayan da ya gano cewar amaryar tasa ba budurwa ba ce. Kamar yadda labarin yazo a shafukan sada zumunta, mutumin ya fada tarkon amaryar tasa ne inda ta nuna masa fa ita cikakkiyar budurwa ce ashe abin ba haka bane.

Yarinyar ta kasance mai hankali

Ko da yake wanda ya yada labarin a shafin Twitter shima ya bada shaidar cewa yarinyar tana da hankali, sai dai angon ya kasa daurewa bayan ya gano irin karyar data shimfida masa kafin auren su.
Tuni dai aka mayar wa mutumin kudaden da ya kashe a lokacin hidimar auren.

Ga yadda sakon yazo a shafin twitter:

@ChukwuSomma ya rubuta: “Wata ‘yar unguwarmu an maida kudin auren ta sannan kuma an kwaso kayanta zuwa gidan mahaifinta saboda karyar da ta yi wa mijinta cewa ita budurwa ce, auren watan shi 4 kacal ….ashe har yanzu maza na wannan abun?? Omo!”

Kadan daga cikin martanin masu amfani da shafin twitter

@FunmiKolz ya ce: “Me ya sai bayan wata 4 sannan zai korota gidan iyayenta?”

@MEzulike ya ce:”to ita meyasa zatayi karya, shi mutumin dole sai budurwa ne ya ke nema saboda abin ya,kullemin kai.

@sakwaofkigali ya ce: “A gaskiya abin ya burge har mijin ya iya zama da ita har wata 4 Hakan ya kara nuna yadda matar ta kasance maƙaryaci shi kuma mutumin ya kasa ci gaba da hakuri Budurwa.”
Tabdi dama mata har yanzu suna wannan karyar? Shikuma mijin da ya,yi hakuri ya yafe mata sai dai kuma idan akwai wata matsalar bayan wannan.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe