24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Kabilar Himba: Wacce namiji ke karrama bakonsa ta hanyar ba shi danin matarsa don more dare

LabaraiAl'adaKabilar Himba: Wacce namiji ke karrama bakonsa ta hanyar ba shi danin matarsa don more dare

Can yankin Kunene da Omusati da ke arewacin Namibia, akwai wasu jama’a makiyaya ‘yan kabilar Ovahimba da Ovazimba, Pulse.ng ta ruwaito.

A al’adarsu, a ko wacce rana mace za ta dinga tatsar nonon shanu tare da kulawa da yara, yayin da mazan su ke fita farauta har su dauki tsawon lokaci.

Iyayensu maza ne ke zabawa mata mazajen aure

Akalla sun kai mutane 50,000 a yankin kuma su na auren mata fiye da daya yayin da ake aurar da ‘yan matan Himba ga mazajen da iyayensu su ka zaba musu da zarar sun kai munzalin balaga.

Sai dai yanzu sun rage wasu daga cikin al’adunsu saboda zuwan boko yankin.

Amma a ka’idar kabilar, namiji ne kadai mai zabi. Mace kuwa kusan za a ce ba ta da ta cewa da rayuwarta. Wajibi ne ta yi biyayya ga mijinta.

Kamar yadda The Guardian ta ruwaito, idan aka yi bako namiji, ana karrama shi ne ta salon Okujepida Omukazendu – wato namiji ya bar wa bakon danin matarsa da dare yayin da mijin zai koma wani dakin na daban.

Idan kuma babu daki, wajibi ne ya hakura ya kwana a waje.

Su na yin hakan ne don kishin maza ya ragu sannan a gwada juriyarsu.

Su na sanya dokar hana wanka

Dayar al’adarsu wacce yanzu aka dena yin ta ita ce dokar haramta wanka.

Maimakon mata su yi amfani da ruwa wurin wanka, su na turara jininsu ne yayin da su ke shafa wani mai na musamman(kalar ja).

Sun yarda da cewa jar fara tana da matukar kyau da daukar hankali kuma sun yarda da cewa man da su ke shafawa ya na kare su daga rana da cizon kwari.

Mutanen Himba ba su wani samu damar shiga littafan tarihi da al’adun nahiyar Afirka ba.

Ƙabilar Latuka: a wannan kabila, dole ne namiji ya sace duk matar da yake son aure daga baya sai ya sanar da mahaifinta

Yayin da a wasu sassan duniya, dole ne namiji ya fara neman yardar matar da yake son ya aura sannan ya ci gaba da neman amincewar iyayenta, al’ada ta sha bamban a garin Latuka na ƙasar Sudan ta Kudu.

A wannan ƙabilar, dole ne namiji ya sace duk wata ƙyaƙƙyawar mace da yake so sai ya sanar da mahaifinta daga baya
bisa al’adarsu, dole ne mai neman aure ya sace matar da zai aura, ta hanyar daukar wasu mazaje tare da wanda zai yi kwanton bauna, korarsu da kama matar.

Ana kai matar da aka kama zuwa gidan mai neman ta inda ake ajiye ta ba tare da son ran ta ba kafin mutumin ya sanar da mahaifinta daga baya.

Kamar dai duk waɗannan ba su da sha’awa sosai, dole ne mahaifin matar ya yi wa surukinsa duka don ya nuna cewa ya amince da auren da ya yi da ‘yarsa.

Idan mahaifin yarinyar ya amince da wannan mai neman auren ‘yar sa, ana sa ran ya yiwa surukinsa duka shaidar nuna amincewarsa.

Rahotanni sun ce wannan duka na nuni da cewa namijin ya yarda a yi masa dukan tsiya domin matarsa ​​tun da ya shafi sadaukarwar da ya ke son yi wa matar da yake so.

Hakanan abin idan amsar uban ta kasance “a’a”, mai neman yana da ikon yanke shawarar ko zai dawo da ‘yar da aka sace ko kuma ya ci gaba da aurenta ba tare da la’akari da shi ba.

Wannan al’ada mai ban sha’awa ta kasance batun muhawara kuma yana ci gaba da kasancewa kamar yadda mutane da yawa ke ganin cewa gaba ne ga ‘yancin yarinya ta zaɓi wanda take so da kuma son ci gaba da rayuwarta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe