27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Dalilin da yasa ba zan goyi bayan takarar shugaban ƙasa ɗan Arewa a APC ba – Gwamna Lalong

LabaraiDalilin da yasa ba zan goyi bayan takarar shugaban ƙasa ɗan Arewa a APC ba - Gwamna Lalong

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace yana goyon bayan neman takarar shugaban  ƙasan da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yake yi inda ya bayyana cewa ba zai goyi bayan wani ɗan takara daga yankin arewacin Najeriya ba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Lalong ya bayyana hakan ne a Jos lokacin da Amaechi yaje jihar domin neman ƙuri’un deliget din jihar kafin zuwan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.

Lalong ya bayyana taimakon da Amaechi yayi wa jihar Filato

Lalong yace Amaechi ya taimaka wa jihar Filato matuƙa gaya saboda haka mutanen jihar suna tare da shi, ciki harda tsofaffin shugabannin majalisar jihar da ‘yan majalisa masu ci a yanzu.

A wata sanarwa da Lalong ya fitar ranar Asabar, gwamnan yace:

Amaechi yana dukkanin halayen shugaba nagari, zai ceto ƙasar nan daga matsalar tsaro, sannan ya kawo cigaba a dukkamin yankunan ƙasar nan, jihar Filato tanamfana sosai da Amaechi, saboda haka yanzu lokacin ramawa kura aniyar ta ne

Lalong ya jaddada cewa Amaechi zai iya magance matsalar tsaro a ƙasar nan, domin yana da alaƙa da masana a fannin tsaro.

Gwamnan yayi nuni da cewa Amaechi ya taimakawa jiga-jigan APC a arewacin Najeriya, musamman a jihar Filato, domin yin rajista da jam’iyyar. Ya ƙara da cewa tsohon minista ya taimaka wajen ganin jihar ta samu manyan ayyuka daga gwamnatin tarayya

Ubanmu ɗaya da Amaechi, ba zan iya takarar Shugaban ƙasa da shi ba – Inji gwamna Badaru

A wani labari na daban kuma, gwamnan jihar Jigawa, Badaru, yace ba zai iya ƴin yaƙara da Amaechi ba saboda ubansu ɗaƴa.

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, a jiya ya bayyana cewa, ba zai yi takarar Shugabancin kasa ba matukar dai tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi yana yin takara domin neman kujerar. Jaridar The Nation ta rahoto

Ya bayyana hakan ne, yan kwanaki kafin Amaechi din ya dawo da fam din takarar da kuma nuna muradinsa na tsayawa takarar a hedikwatar uwar jamiyyar dake Abuja.

Badaru ya bayyana hakan ne, yayin da Amaechin ya kai ziyarar karamar tattaunawa da wakilan deliget, gabanin ranar 29 ga watan Mayu, wacce za’a gabatar da zaɓen fidda gwani na shugaban kasa a jamiyyar ta APC.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe