28.2 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

TSARO: Gombe ta ƙara bayyana a jiha mafi kwanciyar hankali a Najeriya

LabaraiTSARO: Gombe ta ƙara bayyana a jiha mafi kwanciyar hankali a Najeriya

Jihar Gombe, ta kasance jiha mafi aminci a Najeriya a cikin rubu’in farko na shekarar 2022, Vanguard ta ruwaito.

Rahoton da Statisense ya fitar a shafinta na yanar gizo da kuma tabbatar da shafinta na Twitter (www.statisense.com.ng) wanda ya nakalto Nigeria Security Tracker, ya ce an samu rahoton mutuwar mutane 3,859 da kuma yin garkuwa da mutane 1,827 a cikin watanni huɗu na farkon shekarar 2022 yayin da jihar Gombe ta ce babu lamarin satar mutane da kuma mutuwar mutum ɗaya kawai.

gombe
TSARO: Gombe ta ƙara bayyana a jiha mafi kwanciyar hankali a Najeriya

Statisense kamfani ne na fasahar bayanai wanda ya ƙware wajen samar da sahihin bincike da rashin son zuciya a fagage da dama a Najeriya, wadanda suka hada da tattalin arziki, kasuwanci, tsaro, da sauransu.

Sauran jihohin da ke ƙarƙashin wannan rukuni sun haɗa da; Nasarawa, Adamawa, Ekiti, da Bauchi da aka fi samun rahotannin sace-sace da mace-mace.

Rahoton ya yi nazari kan laifukan da suka haɗa da yin garkuwa da mutane da kuma wasu munanan laifuka da suka yi sanadin mutuwar mutane.

Idan dai za a iya tunawa, a wani rahoto makamancin haka a watan Janairun wannan shekara, wanda Eons Intelligence, wata kafar yada labarai, leken asiri da bayar da shawara ta Eons Intelligence ta buga, an bayyana Gombe a matsayin ɗaya daga cikin jihohin ƙasar nan mafi zaman lafiya. Eons Intelligence ta ƙware wajen nazarin laifuka, siyasa, kasadar tattalin arziki da dama a Najeriya.

Har ila yau, taron Daraktocin Tsaro na Jihohi (SDS) a shiyyar Arewa maso Gabas, ya ayyana Gombe a matsayin Jihohin da suka fi zaman lafiya a yankin kuma ɗaya daga cikin mafiya zaman lafiya a ƙasar nan.

Gwamna Muhammadu Inuwa tun daga hawan gwamnatinsa ya mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, alƙawarin guda ɗaya da ya sa jami’an tsaro suka karɓe shi a matsayin babban jakadan Peqce da tsaro da zaman lafiya a ƙasa.

Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya taɓa bayyana Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin shugaba mai gaskiya, mai kishin ƙasa, mai riƙon amana kuma mai tsayin daka mai kishin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jiharsa da Najeriya.

Abin Al’ajabin Falakin Gombe ya bayyana inda ya samo abubuwan da ya yi amfani da su wurin hawan Sallah

Abin Al’ajabin Falakin Gombe ya magantu dangane da hawan da ya yi har ya dauki hankalin mutane da dama, kuma da alamu ba mutum ba ne, Aminiya ta ruwaito.

Yayin da ko wanne gari ya ke baje al’adunsu na gargajiya wurin bikin sallah, hawan garin Gombe ya dauki hankali kwarai.

Kasancewar wannan ne karo na farko da jama’a su ka makamanciyar shigar Abin Al’ajabi, wanda ya taho cikin tawagar Falakin Gombe.

Aminiya ta samu damar tattaunawa da Abin Al’ajabin Falakin Gombe wanda ya bayyana inda ya samo duk abubuwan da ya yi amfani da su wurin hawa.

A cewarsa, daga duniyarsu ya samo komai kuma a Gombe kadai zai iya hawa don Falakin Gombe kadai ya sani.

Ya ce ta yuwu ya sake dawowa a wata sallah don yin hawa. Amma babu tabbas. Ya ce sai abinda Allah ya yi.

Mutane da dama sun razana yayin da wasu kuma ya burgesu da irin shigarsa tare da yadda ya dinga sarrafa halittu da kuma doki wanda wasu ke ganin kamar da tsafi akansa.

Babu shakka a wannan shekarar, babu wani basarake da hawan sa ya dauki hankali fiye da ta Falakin Gombe kasancewar Abin Al’ajabi yana tawagarsa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe